• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

bySulaiman and CGTN Hausa
3 weeks ago
Jagorancin duniya

Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da Shawarar inganta jagorancin duniya, wato Global Governance Initiative a turance, a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai. Wannan shawara ta shafi tabbatar da daidaito tsakanin kasashe daban daban, da bin ka’idoji wajen kula da harkokin kasa da kasa, da daukaka manufar cudanyar sassa mabambanta, da dora muhimmanci kan kare moriyar jama’a, da kuma kokarin neman hakikanin sakamako. Ta kuma wakilci muradun dimbin kasashe masu tasowa, ta yadda ta samu yabo da goyon baya daga kasashe daban daban. Cikinsu kasar Najeriyar ta ce wannan shawara wani tsari ne mai kima na raya wasu muhimman ayyuka, da manufofin raya kasa na tarayyar Najeriya da ajandar kungiyar kasashen Afirka ta 2063 suka kunsa.

To, ko me ya sa kasar Sin ta gabatar da shawarar a wannan lokaci da muke ciki? Dalili shi ne a bisa sauye-sauyen yanayin kasa da kasa, tsarin kula da harkokin duniya da kasashen yamma ke jagoranta ya kusan daina aiki.

  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

A cikin ‘yan shekarun nan, yayin da kasashen yammacin duniya ke fama da matsalolin da suka hada da tafiyar hawainiya a fannin tattalin arziki, da ja-in-ja na harkokin siyasa, da tsanantar kabilanci, da yake-yake, sun kara zama marasa daukar alhaki a al’amuran kasa da kasa.

Wani babban misali a wannan fanni shi ne kasar Amurka. Wannan kasa wadda ta kasance mafi girma a cikin kasashe masu sukuni, ta zama ta farko a fannin yin watsi da ka’idojin kasa da kasa. Ba ma kawai ta sha ficewa daga yarjeniyoyin da kungiyoyin kasa da kasa suka kulla ba ne, har ma ta rage tallafin da take bayarwa ga kasashen ketare, da kin biyan kudin da ya kamata ta biya ga Majalisar Dinkin Duniya bisa matsayinta na mambar majalisar, kana sau da dama ta hana Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zartar da kudurorin da za su iya tabbatar da adalci a al’amura daban daban.

LABARAI MASU NASABA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai na al’ummar kasashe masu tasowa. Ta haka za mu san cewa gyara ya riga ya wajaba.

Saboda haka, shawarar inganta jagorancin duniya ta zama wani abun dake biyan bukatun dake akwai a duniyarmu. Wannan ya sa ta samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.

Ta wannan shawara ta inganta jagorancin duniya, za mu iya kara fahimtar halayyar kasar ta Sin. Ko da yake wani yanayin da duniyarmu ke ciki shi ne dishewar tauraron kasashen yamma, amma duk da haka, kasar Sin ba ta neman yin koyi da kasashen yamma wajen yin babakere a duniya. Tana neman gyara, da inganta tsare-tsaren kula da harkokin duniya, ta yadda za ta tabbatar da moriyar dukkan kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, maimakon kafa wani sabon tsari da ya saba wa tsarin kasa da kasa na yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar diflomasiyya, shi ne kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama, da kokarin tabbatar da ci gaban harkokinsu na bai daya.

Yayin da karin kasashe ke nuna goyon bayansu ga shawarar kula da al’amuran duniya da kasar Sin ta gabatar, tabbas za mu shaida hadin gwiwar karin mutane a duniya don neman wanzar da adalci, abin da zai haifar da damar tabbatar da daidaito da adalci a duniyarmu. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version