• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Kwalejin Noma Da Duba Aikin Babban Asibitin Maradun

by Leadership Hausa
1 year ago
gwamna

A ci gaba da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da manyan ayyuka biyu a Ƙananan Hukumomin Bakura da Maradun da ke yankin Zamfara ta Yamma.

Manyan ayyukan na cikin waɗanda Gwamnatin Dauda Lawal ta aiwatar cikin shekara guda.

A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa gwamnan ya ziyarci ƙananan hukumomi uku: Mafara, Bakura, da Maradun.

A Ƙaramar Hukumar Talatan Mafara, Gwamna Lawal ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda ya sami babban asibitin ƙaramar hukumar a lalace.

“A yau, a ci gaba da ƙaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a shekarar farko da Gwamna Lawal ya yi kan mulki, Gwamnan tare da rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, sun ƙaddamar da sabuwar Kwalejin Noma da Fasaha da aka gyara a garin Bakura.”

LABARAI MASU NASABA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Ƙananan Hukumomin Zamfara

A jawabinsa wajen ƙaddamar da kwalejin, Gwamna Lawal ya ce; sama da shekaru ashirin da kafa Kwalejin Noma ta Bakura, tsarinta ya lalace, inda ba za a iya koyo ko koyarwa a muhallin ba.

gwamna

“A matsayinmu na gwamnatin da ta bayyana ilimi da noma a cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba, mun ga ya dace a gyara kwalejin tare da adana mata muhimman abubuwan da za a samar da ingantaccen ilimin aikin gona.

“Mun kuma ɗaga darajar Cibiyar daga Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi zuwa Kwalejin Noma da Fasaha ta Bakura. Hikimar da ke tattare da wannan ita ce bai wa kwalejin damar gabatar da wasu fasahohi a matsayin abin da ake buƙata don sauye-sauyen ɗaga fasahar zamani a kwalejin.

“Saboda haka, a yau mun taru a nan domin ƙaddamar da ayyukan gyare-gyaren da aka gudanar a kwalejin. Waɗannan sun haɗa da gyara ɓangaren masu gudanarwa, ɗakin gwaje-gwajen iri da sauran abubuwan da suka shafi noma, ɗakin gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta, ɗakin gwaje-gwajen abubuwan da suka shafi kimiyya, babban ɗakin lakca da ɗakunan kwanan ɗalibai. Har ila yau, an gina wasu bankunan manyan baƙi guda biyar tare da inganta tsarin ruwa na kwalejin.”

Yayin da yake a ƙaramar hukumar Maradun, Gwamna Lawal ya yi dubi da yadda ake gudanar da aikin gyaran babban asibitin Maradun.

gwamna

“Kwangilar aikin ta haɗa da gyaran ɓangaren masu gudanarwa, ɗakunan majiyyata maza da mata, ɗakunan kwana na ma’aikata, ɗakin ajiyar gawa, babban ɗakin tiyata, da banɗakuna guda biyu. Sauran ayyukan sun haɗa da katange asibitin, samar da isasshen ruwa na asibitin, hanyoyin tafiya da kayan aiki gaba ɗaya.”

A ƙaramar hukumar Talatan Mafara, gwamna Lawal ya nuna rashin gamsuwa da rashin jin daɗin sa a kan halin da babban asibitin Talatan Mafara yake, inda nan take ya bada umarnin gyara da inganta shi.

“Akwai matuƙar tada hankali ganin halin da babban asibitin Talatan Mafara ke ciki. Ba zan lamunci irin halin da na ga asibiti a ciki ba a lokacin bincike na. Abin da ke nuni da yadda ’yan siyasarmu ke karkatar da dukiyar ƙasa, waɗanda galibi suke aiwatar da al’amura marasa muhimmanci.

“Na ba da umarnin gyara da inganta asibitin nan take. Za mu samar da kayan aikin asibitin don samar da gyara da kuma zama babban jigo ga sauran cibiyoyin kiwon lafiya a yammacin jihar. Inganta yanayin sa zai samar da tsayayyen kiwon lafiya a yankin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano
Labarai

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
Manyan Labarai

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Next Post
NLC Ta Bukaci A Kara Wa ‘Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho

NLC Ta Bukaci A Kara Wa 'Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho

LABARAI MASU NASABA

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari 

November 7, 2025
An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.