• English
  • Business News
Tuesday, May 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto and Sulaiman
7 months ago
in Ra'ayoyi
0
Shekara 64 Da Samun ‘Yanci: Maimakon Biki, Jajantawa Ya Kamata A Yi – ‘Yan Nijeriya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yayin da Nijeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, ‘yan kasa da dama na bayyana ci-gaban da aka samu a tsayin wadannan shekarun a matsayin ci-gaban mai hakar rijiya kansancewar har yau kasar ba ta tsayu da kafafun ta ba ballantana ta kai matakin da ya kamata ta kai.

 

Tun bayan samun ‘yan cin kai a ranar 1 ga Oktoba 1960, Nijeriya ta fuskanci kalubale da dama da suka hada da kwan- gaba- kwan- bayan mulkin soji, fafutukar tabbatar da mulkin dimokuradiyya, siyasar yanki, rikita- rikitar addini da kabilanci da kuma gagarumar matsalar tsaro daga Kudu zuwa ArewaMafi yawan al’ummar Nijeriya na bayyana shekaru 64 na ‘yancin kai a matsayin shekarun gurbataccen mulki, shekarun mulkin danniya da zalunci, cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro, rugujewar tattalin arziki kana shekaru 64 na satar danyen mai, rashin wutar lantarki, koma baya a sha’anin ilimi, aikin gona da rashin ayyukan yi tare da hauhawar farashin mai da tsadar rayuwa.

  • APC Ta Lalata Nijeriya, PDP Kuma Matacciyar Jam’iyya Ce — Kwankwaso
  • Kirkirar Kimiyya Da Fasaha Ta Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Akasin murnar samun ‘yancin kai, kungiyoyin farar hula da na matasa da dalibai sun gudanar da zanga-zangar kira ga gwamnati a kan ta gaggauta shawo kan matsalolin tsadar rayuwa, rage farashin mai da bunkasa tattalin arziki wadanda suka zama silar jefa al’umma a cikin kunci musamman a dalilin cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati masu tsauri.

 

Labarai Masu Nasaba

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

A cewarsu maimakon shagalin biki, kamata ya yi a yi zaman jajantawa juna kan gurbatacciyar hanyar da shugabannin kasar mabambanta suka hau na rashin ci-gaba akasin ingantacciyar hanyar da shugabannin baya wadanda suka jagoranci samarwa kasar ‘yanci suka dora ta a kai.

 

Zanga-zangar wadda ta gudana a Birnin Tarayya Abuja da Lagas a karkashin jagorancin matashin dan gwagwarmaya, Omoleye Sowore sun bayyana cewar ba a bukatar gudanar da wani shagalin buki a wannan ranar illa gwamnati ta shawo kan tsananin halin da al’umma suke ciki wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kafuwar kasar bakidaya.

 

Sai dai a jawabin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyanawa al’ummar kasa cewar yana sane da halin da suke ciki na tsadar rayuwa, yunwa da rashin ayyukan yi don haka ya baiwa al’umma hakuri da cewar al’amurra za su daidaita duk da a cewarsa tsadar rayuwar lamari ne da ya shafi duniya bakidaya.

 

Haka ma Tinubu ya bukaci karin lokaci kan tsare- tsaren da gwamnatinsa ta assasa wadanda ‘yan kasa ke kuka da su wadanda suka yi tasiri wajen haifar da tsadar rayuwa da yunwa yana cewar nan da dan lokaci al’umma za su dara. Ya ce yana da tabbacin za a samu wadataccen abinci kuma a cikin farashi mai sauki yana cewar alkawali ne wanda ba zai saba ba.

 

Ya ce ya karbi mulkin kasar nan a wani mawuyacin yanayi na matsalolin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki wanda ba su da wani zabi face gudanar da sauye- saye domin magance matsalolin ko kuma a ci-gaba da tsarin da suka tarar wanda zai sa kasar ta durkushe wanda a kan hakan suka zabi yin sauye- sauye a fannin tattalin arziki da tsaro a inda suka samu nasarar yakar Boko- Haram da ‘yan ta’adda.

 

A yayin da yi waiwayen baya kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu ya bayyana cewar a sakamakon tsare- tsaren da gwamnatinsa ta assasa, ‘yan kasar waje sun zuba jarin makuddan kudade har dala biliyan 30 a Nijeriya.

 

Ya ce a tsawon shekarun da Nijeriya ta yi da samun ‘yancin kai an cimma wasu burikan wadanda suka yi fafutukar samarwa kasar ‘yanci shekaru 64 da suka gabata. Ya ce ‘yan Nijeriya sun zama abin koyi da alfahari a fannoni daban daban kuma kullum kara samun ci-gaba ake yi.

 

A cewarsa Nijeriya a yau ta dauki darasi a bisa ga kura- kuran da aka tafka a baya ta yadda ta ci-gaba da dorewa a matsayin kasa daya dunkulalliya duk da yakin basasa da sauran rikice-rikice da bambance- bambance da matsalolin da aka yi ta fama da su a cikin shekaru 64 da samun ‘yancin kai.

 

Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar jawabin shugaban kasa cike yake da alkawulan da aka kasa cikawa, nasarorin karya da yaudarar ‘yan Nijeriya kamar yadda sakataren yada labarai na jam’iyyar, Debo Ologunaba ya bayyana a jawabin da ya sanyawa hannu a muhimmiyar ranar.

 

A cewar jam’iyyar, jawabin shugaban kasa ya kasa magance muhimman lamurra ko samar da mafita ga dimbin matsalolin tattalin arziki da tabarbarewar tsaro da ake fuskanta ta na cewar kawai an rubuta jawabin ne domin ci- gaba da yaudarar ‘yan Nijeriya a bisa ga gazawar gwamnatin APC.

 

Jam’iyyar ta ce sauraren jawabin shugaban kasa bata lokaci ne kawai domin ya kasa sanar da hanyoyin magance halin kuncin da al’umma suke ciki. A cewar jam’iyyar kasawar Tinubu wajen bayyana rage farashin man fetur da daga darajar naira ya nuna yadda gwamnatinsa ke nuna halin ko- -in- kula ga mummunan halin da ‘yan kasa suke ciki wanda hakan ya tabbatar da cewar babu wani abu da za a yi tsammani a gwamnatin mai ci.

 

A jawabin jagoran ‘yan adawar Nijeriya, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘yan kasa bisa jajircewa ta yadda da Nijeriya a matsayin kasarsu ta gado.

 

“A wannan rana a yayin da muke cika shekara 64 da mallakar ‘yancin mu ina alfahari da kafuwar mulkin dimokradiyya haka kuma wannan rana na tunatar da mu shekaru mafi tsayi na mulkin dimokuradyya a tarihin wannan kasa.”

 

Dan takarar na shugabancin kasa a zaben 2023 a jam’iyyar PDP, ya jaddada cewar a yayin da hukumomin kasar nan ke aiki da manufa irin ta dimokuradiyya kamar yadda yake a kunshe a cikin tsarin mulkin Nijeriya har a yanzu akwai sauran rina a kaba wajen bawa kowa damar da ta dace a siyasance da kuma tabbatar da aiwatar da zabe na adalci.

 

Atiku ya bayyana cewar a na tafiyar da salon dimokuradyyar kasar nan a salon kama- karya don haka ya bukaci hadin kan jagororin siyasar Nijeriya nan domin daidaiita alkiblar siyasar kasar nan.

 

Ya ce tsarin da ake a kai a yanzu yana haifar da gurbatattun zabuka ta yadda wadanda ke a kan mulki ke amfani da karfin iko wajen danne zaben al’umma. Ya ce baya ga rikicin zabe haka ma a na ci- gaba da murkushe jam’iyyun adawa tare da raunata su a yayin da jam’iyyar da ke kan madafun iko ke ci-gaba da amfani da karfin mulki wajen cin karensu ba babbaka.

 

“Sannu a hankali kasar na karkata zuwa tsarin jam’iyya daya wanda ya zama wajibi ga dukkanin ‘yan siyasa da masu kishi da sauran dattawan kasa da a tashi tsaye wajen yakar wannan barazana. Don haka ina kria ga ‘yan siyasa da su zo mu hadu ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba mu samar da jam’iyyar adawa mai karfin da za ta kai ‘yan Nijeriya ga- gaci.” ya bayyana.

 

A fafutukar samarwa Nijeriya ‘yancin kai wanda ya tabbata a ranar 1 ga Oltoba 1962, jajirtattun mutane da dama sun taka muhimmiyar rawar ganin Nijeriya ta fta daga kangin bautar turawan mulkin mallaka.

 

Wasu daga cikin wadanda suka yi fice a gwagwarmayar samun ‘yancin kai sune; Sa Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) cif Anthony Enahoro, Herbert Macaulay, cif Obafemi Owolowo, Funmilayo Ransom Kuti, Nnamdi Azikiwe da Sa Abubakar Tafawa Balewa wanda shine firamin ministan Nijeriya na farko bayan samun ‘yancin kai da sauransu da suka nuna jarumta da kishin kasa a fafutukar ganin Nijeriya ta tsayu da kafafun ta.

 

Sai dai ‘yan kasa da dama na da ra’ayin Nijeriyar da jagororin tabbatar da ‘yancin kasar nan suka samar ba ita ba ce a yanzu, musamman a bisa ga yadda shugabannin ta suka kauce wajen wanzar da mulkin gaskiya da adalci tare da kishin kasa a matsayin kasa daya al’umma daya irin yadda magabata suka dora ta a kai.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: 'Yancin KaiDimokuradiyyaNijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

APC Ta Lalata Nijeriya, PDP Kuma Matacciyar Jam’iyya Ce — Kwankwaso

Next Post

Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba

Related

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

2 months ago
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

6 months ago
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

7 months ago
Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
Ra'ayoyi

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamnatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano

7 months ago
Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai
Ra'ayoyi

Dauda Lawal A Shekara 59: Mai Gidana Wanda Bai Da Jiji Da Kai

8 months ago
Yanci
Ra'ayoyi

Matsalar Kifewar Kwale-kwale A Jihar Jigawa

9 months ago
Next Post
Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba

Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba

LABARAI MASU NASABA

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

May 13, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 

May 13, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Tambarin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Murkushe Harin Japan

Kasar Sin Ta Fitar Da Tambarin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Murkushe Harin Japan

May 13, 2025
Wata Mata Ta Kashe Dan Hayar Da Ke Gidanta A Ondo

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m

May 13, 2025
Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa

Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.