ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus

by Khalid Idris Doya
18 hours ago

Babban Kwamishina mai kula da sashen Hisbah ta hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi, Barr. Aminu Balarabe Isah, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Isah ya sanar da ajiye aikinsa ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 26 ga Oktoba, 2026, wadda ya aikawa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.

A cikin wasiƙar, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne a ƙashin kansa kuma ya yi hakan ne bisa raɗin kansa, yana mai jaddada cewa matakin ba shi da alaƙa da wata takaddama tsakaninsa da gwamnatin jihar ko wani jami’in gwamnatin.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ina rubuto muku wannan wasiƙa ne domin sanar da ku a hukumance game da matakin da na yanke ta yin murabus daga muƙamina na Kwamishina na dindindin mai kula da Hisbah a ƙarƙashin Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi.”

Ya ƙara da cewa ya yanke wannan shawara ne bayan zurfin tunani, kuma ba wani saɓani da gwamnati ne ya jawo hakan ba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

“Na yanke wannan shawara ne bayan yin nazari sosai, kuma mataki ne da ya shafi ƙashin kaina zallah. Ina son in bayyana a sarari cewa murabus ɗina na bisa raɗin kaina ne gaba ɗaya, kuma ba shi da alaƙa da wata taƙaddama ko matsala tsakanina da gwamnatinku ko wani jami’i a cikin gwamnatinku.

“Ina barin wannan matsayi ne cikin cikakken girmamawa ga tsarin gwamnati da kuma mutanen da na samu damar yin aiki tare da su,” In ji shi.

Tsohon kwamishinan ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Mohammed bisa ba shi damar yin hidima a gwamnatinsa.

Ya bayyana naɗin da aka yi masa a matsayin babban abin alfahari, yana mai cewa yana matuƙar godiya bisa amincewar da aka yi da shi wajen jagorantar sashen Hisbah, wanda ya bayyana a matsayin sashe mai matuƙar muhimmanci.

Ya ce, “Babban abin alfahari ne a gare ni na bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kyawawan ɗabi’u da ci gaban Jihar Bauchi ta hannun sashen Hisbah. Ina matuƙar godiya bisa amincewar da kuka yi da ni ta hanyar naɗa ni a wannan muƙami mai muhimmanci kuma mai matuƙar kulawa.”

Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    2027: Mazauna Bauchi Sun Ƙalubalanci Iƙirarin Limami Na Cewa An Cire Shi Saboda Tallar Tinubu
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Rikicin Cikin Gida Ya Ɓarke A Jam’iyyar APM, Wani Ɓangare Ya Tsige Shugaban Jam’iyyar A Bauchi

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

October 27, 2026
Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda
Manyan Labarai

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

October 27, 2026
IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya
Labarai

IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

October 27, 2026
Next Post
Tinubu Ba Shi Da Ƙwarewa Da Lafiyar Da Zai Jagoranci Nijeriya – Obi

Tinubu Ba Shi Da Ƙwarewa Da Lafiyar Da Zai Jagoranci Nijeriya - Obi

LABARAI MASU NASABA

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

Hada-Hadar Yawon Shakatawa A Cikin Gidan Sin Ta Bunkasa Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2026
An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

An Kaddamar D Cibiyar Confucius Ta Dijital Da Fasaha Ta Jami’ar Mulungushi A Zambiya

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata

October 27, 2026
ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya

October 27, 2026
An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

An Kaddamar Da Taron Kirkire-Kirkire Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Na Ziri Daya Da Hanya Daya A HK

October 27, 2026
Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

Kungiyar JIBWIS Ta Miƙa Ɗan Agajin Da Ake Zargi Da Kalaman Ƙiyayya Ga Ƴansanda

October 27, 2026
IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

IRENA: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Wajen Sauyin Makamashi A Duniya

October 27, 2026
Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

October 27, 2026
Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki

Sin Na Ci Gaba Da Jan Zare A Fannin Bunkasa Hanyoyin Sufurin Jiragen Kasa Da Habbaka Tattalin Arziki

October 27, 2026
INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

INEC Na Fuskantar Suka Kan Amfani Da Manhajar AI

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.