Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce Shugaba Bola Tinubu da lafiya da ƙwarewar da ake buƙata domin magance matsalolin Nijeriya.
Da yake jawabi a wani taron jam’iyyar a Abuja ranar Litinin, Obi ya ce ’yan Nijeriya na buƙatar sabon shugabanci.
Ya kuma yi gargaɗi kan maguɗin zaɓe a babban zaɓen 2027, yana mai kira da a gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Obi ya kuma yi Allah-wadai da zargin cin zarafin magoya bayansa, yana mai cewa bai kamata a ɗauki son zaman lafiya a matsayin gazawa ba.
Shugaban jam’iyyar NDC na ƙasa, Moses Cleopas, ya buƙaci ’yan jam’iyyar su mara wa dukkanin ’yan takararta baya a zaɓen 2027.
Ya yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wanda aka samu da aikata abin da ya saɓa wa muradun jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Seriake Dickson, ya ce an kafa NDC ne domin samar da wata jam’iyyar da za ta zama madadin jam’iyyar APC mai mulki.
Ya zargi APC da gaza cika alƙawuran da ta yi kan tsaro, yaƙi da cin hanci da rashawa, da farfaɗo da tattalin arziƙi.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa ta samu kuɗaɗen shiga har naira biliyan 8.53 cikin watanni takwas da aka yi mata rajista, inda ta ce naira biliyan 6.13 ne suka rage bayan cire kuɗaɗen da aka kashe.
NDC ta kuma buɗe sabon hedikwatarta a Abuja tare da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.
Sai dai ƙungiyar Obi-Kwankwaso Movement ta soki jam’iyyar kan sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta a makare, tare da nuna shakku kan ƙarfinta a matakin ƙasa da shirinta na tunkarar zaɓen.














