Shirye-shiryen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugabancin ƙasa jam’iyyar APM, Injiniya Seyi Makinde, da abokin takararsa, Lawal Daura a jihar Bauchi sun kankama.An tsara gudanar da taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamba, 2026, a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa Memorial Stadium (ATBS), da ke tsakiyar birnin Bauchi.
Ana sa ran taron zai samu halartar ɗimbin mambobin jam’iyyar APM, magoya bayanta da masu ruwa da tsaki a harƙoƙin siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar nan, yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙara ƙarfafa yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa.
Kazalika, taron zai zama wata dama ga ɗan takarar shugaban ƙasa da abokin takararsa wajen gabatar da yunƙurin da suke da su na farfaɗo da ƙasar nan, tare da bayyana manufofinsu da hangen nesansu na gina Nijeriya.
Kafin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen, ana sa ran Makinde zai tattauna kai tsaye da ’yan Nijeriya ta hanyar shirin hirar kai tsaye a gidan rediyon Bauchi Radio Corporation (BRC).An tsara gudanar da shirin, wanda za a kuma watsa kai tsaye a kafafen sada zumunta na gidan rediyon, a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2026, tsakanin ƙarfe 6 na yamma zuwa 8 na dare.
Shirin zai bai wa masu sauraro damar gabatar da tambayoyinsu tare da jin kai tsaye daga ɗan takarar shugaban ƙasar kan tsare-tsarensa, manyan abubuwan da zai bai wa fifiko da ajandarsa ga Nijeriya gabanin zaɓen shekarar 2027.
Ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen zai zama wani gwaji na farko da zai nuna ƙarfin jam’iyyar wajen tattara magoya baya da gano alamar ko za ta iya kwace mulki a hannun APC ko yaya.













