Shugaban NLC Ya Bayyana Dalilin Yawaitar Matsalar Tsaro A Nijeriya

Matsalar srao

Daga Maigari Abdulrahman,

Shugaban Hukumar kwadago ta kasa, Kwamared Ayuba Wabba, ya ce, gazawar gwamnati ga ‘yan kasa, musamman gwamnatin Jihar Kaduna na daga cikin abinda ke kara rura matsalar tsaro a kasa.

A cewar sa, dayawan mutane kan shiga miyagun harkoki saboda talauci da kangin rayuwa.

Tsawon tarihi a Najeriya, gwamnatoci sun kawo tsare-tsaren koma-baya ga aikin gwamnati, wanda kuma shi aikin yana dai daga cikin hanyoyin da ke kara habbaka kasa tare da yalwatar hanyar arzikin mutane, in ji shi.

A cewar sa, rage kadarin kudin Najeriya da durkushewar naira, ya illata ma’aikatan gwamnati fiye da kowa a kasar, wanda hakan ya kara taimakawa tabarbarewar tsaro a kasar.

Shugaban, da ya ke jawabi a wurin taron manyan malaman kwalejin kimiyu na kasa karo na 3, a Abuja, ya ce Gwamnan Kaduna Nasiru Elrufa’i ne da mafi munin tarihi a Najeriya a kan abinda ya shafi kuntatawa ma’aikata.

Kungiyar kwadago ta zargi Nasiru Elrufa’i da korar malamai dubu 21,000. Da kudin shigar da Jihar ke samu biliyan 50.7, ba zai yiyu su ce ba su iya biyan albashin ma’aikata a mafi karancin 30,000, in ji shi.

Shugaban ya koka kan irin yadda ‘yan siyasa ke alkawarin bogi a lokutan zabe ba tare da cikawa ba domin jan ra’ayin ma’aikata.

Haka kuma, ya koka kan yadda su ke kin cika alkawarin yarjejeniya, wanda ya ce abin mamaki ne da ya ke faruwa a Nijeriya kadai.

Exit mobile version