Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar Sri Lanka a jirgi sama na yaki, a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.
Rundunar sojin sama ta kasar ta tabbatar da cewa shugaban kasar, mai shekara 73, ya tsere zuwa Maldives tare da matarsa da jami’an tsaro biyu.
- An Tsinci Gawar Jarumin Fina-Finan Nollywood, Abuchi Ikpo A Gidansa
- Na Matsu Mulkina Ya Kare Na Sauka – Buhari
Sun isa babban birnin kasar, Male, da misalin karfe 3 na dare, kamar yadda rahotanni suka rawaito.
Tserewar da shugaba Rajapaksa ya yi daga kasar ta kawo karshen mulkin da iyalansa suka kwashe fiye da shekaru 20 suna yi a kasar Sri Lanka.
Shugaban kasar ya buya bayan da dandazon jama’ar da ke zanga-zanga suka mamaye gidansa a ranar Asabar, kuma ya yi alkawarin sauka daga mulki a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli.
Wata majiya ta bayyana cewa Rajapaksa ba zai ci gaba da zama a Maldives ba don haka yana da niyyar zuwa wata kasar.
Dan uwansa, wanda shi ne tsohon Ministan Kudin kasar Basil Rajapaksa, shi ma ya tsere daga Sri Lanka kuma an ce ya nufi Amurka.
A yayin da ‘yan kasar Sri Lanka suka wayi gari da labarin tserewar shugaban kasar, dubban mutane sun bazama kan titunan Colombo, babban birnin kasar.
Da dama daga cikinsu sun taru a Galle Face Green, babban filin da ake gudanar da zanga-zanga a kasar.