Kwamitin jiga-jigan jam’iyyar APC na kasa, ya kammala wani shirin tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Za a amince da nadin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da nadin kakakin majalisar dattawa ta 9, Sanata Ajibola Basiru, a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa a yau a taron majalisar zartarwa na kasa da aka shirya gudanarwa yau a Transcorp Hilton a Abuja.
- Fitaccen Malamin Musulunci Dokta Ismail Surty, Ya Rasu A Birtaniya
- NLC Ta Dakatar Da Zanga-zangar Da Ta Shiga
An tattaro cewa, a taron da suka yi a fadar shugaban kasa a daren jiya, kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta kasa ta umarci shugabannin jam’iyyar da su tsara hanyoyin da za su kawar da duk wani cikas ga tsohon gwamnan a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa a yau.
A cewar majiyoyi, kwamitin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta, ya ce suna sane da wasu matsaloli na shari’a da tsarin mulki, wadanda ka iya zama tarnaki wajen tabbatar da shugabancin Ganduje.
An umarci kwamitin da ya kawar da matsalolin da ka iya zama tarnaki.
A yau ne ake sa ran Ganduje zai karbi ragamar shugabancin jam’iyyar a yayin taron kwamitin zartarwa na kasa.