Tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Igabi ta tarayya daga jihar Kaduna Hon. Ibrahim Bello Rigachikun ya bayyana cewa, katsalandan din bangaren gwamnatin tarayya ne ya janyo turka-turkar da ke faruwa wajen neman shugabanci majalisun tarayyar ta 10 a kasar nan.
Bello, a hirarsa da LEADERSHIP Hausa a Kaduna ya ce, idan kaji ‘yan majalisa na yin korafi, mussaman akan abinda ya shafi tafiyar da harkokin majalisa, to babu shakka, bangaren zartwar ne suka yiwa musu katsalandan.
Ya yi nuni da cewa, ba a yiwa ‘yan majalisa katsalandan, sai dai lallashi da roko a tsakanin ‘yan majalisa a wajen majalisar.
Bello ya ce, misali a majalisar wakilai ‘yan majalisar ne za su zabo wanda suke son ya shugabance su, har azo ayi zaben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp