Wata guguwa da taho tare da ruwan sama a karamar hukumar Misau a cikin jihar Bauchi, ta lalata gidaje Sama da 200.
JaridarLEADERSHIP ta ruwaito cewa, guguwar ta afku ne a yammacin jiya Lahadi.
Daya daga cikin wadanda guguwar ta yaye wa rufin dakunansa mai suna Malam Kawu Mamuda, ya sheda wa wakilinmu cewa, damuwarsa ita ce, inda iyalansa za su kwana, kafin ya gyara rufin dakunan.
Ya ce, guguwar ta taso ne bazato-ba-tsammani inda ta yi awon gaba rufin gidaje wasu kuma har gidanma ta rusa.
Shi ma wani mai suna Bello Abubakar da iftila’in ya afka wa ya ce, duk kudaden da ya tara don gina gidansa, ya yi asarar su, biyo bayan afkawar guguwar a gidan.
Sai dai, ya danganta iftila’in a matsayin lamari ne daga Allah, inda ya ce, asarar na da yawa, guguwar ta lalata gidaje da dama.
A martanin da gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed ya yi a kafarsa ta sada zumunta ta Facebok ya yi kira ga wadanda iftila’in ya afkawa da su dauki kaddara su yi imanin cewa, wannan jarrabawa ce daga Allah.