Connect with us

KASASHEN WAJE

Shugabannin Rasha Da Turkiyya Da Iran Za Su Gana Kan Batun Lardin Idlib

Published

on

Shugabannin Rasha da Turkiyya da kuma Iran zu su yi wani taron koli a birnin Tehran kan batun.
Rasha da Iran kawayen Siriya ne na kud-da-kud kuma su na goyon bayanta ta fuskar soji, a yayin da kuma Turkiyya, wacce ke iyaka da Idlib, ta ke goyon bayan ‘yan tawayen. Turkiyya na fargabar fuskantar matsalar ‘yan gudun hijira muddun sojojin Siriya su ka kai harin.
A halin da ake ciki kuma, Kwamitin Sulhun MDD zai yi wani zama na gaggawa a birnin New York a yau jumma’a kan wannan batu na rikicin Syria.
“Daukar duk wani mataki na soji a Idlib ka iya jefa rayuwar mutane fiyeda milyan uku farar hula cikin hadari, ciki har da yara wajen miliyan daya da ke yankin,” a cewar takardar bayanin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: