Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Caroline Wura-Ola Adepoju, ta yi kira da a ci gaba da hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro don kare iyakokin Nijeriya.
Ta ce ba za a yi watsi da horas da jami’an tsaro ba musamman a yanzu da kalubalen da suka hada da safarar makamai, fashi da makami da sauran munanan dabi’u da ka iya kawo cikas ga tsaron al’ummar kasar nan ke kara ta’azzara.
- Jami’ai 3 Da Sojoji 22 ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Neja -DHQ
- Sojojin Nijar Na Neman Goyon Bayan Kasashe Daban-Daban
Adepoju ta bayyana haka ne a jiya a hedikwatar hukumar a Abuja.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, DCI Aridegbe Adedotun ya fitar, ta bayyana cewa shugabar NIS, ta ce ziyarar da mahalarta taron inganta tsaro 27 suka kai mata wani bangare ne na inganta alaka a tsakaninsu.
Ta ce, “Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kasu gida biyu: tsaron kan iyaka da kula da shige da fice. Amintacciyar iyaka kasa ita samar da tsaro, bukatar NIS shi ne samar da tsaro.
“Kuma tabbas tsaro hakki ne na kowa da kowa, musamman ma kowace hukumar tsaro, shi ya sa aka samar da wannan kwas na tsaro.
“Yayin da ake fama da matsalar rashin tsaro a Nijeriya, fasa-kwaurin makamai, ‘yan fashi da makami, ta’addanci, fadace-fadacen makiyaya da manoma, da safarar kudade da kuma munanan dabi’u, wannan shi ne lokacin da ya dace a bai wa jami’a horo.”
Da yake jawabi a madadin mahalarta taron, mataimakin Kwanturola na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Abubakar Dalhatu Zurumi, ya ce cibiyar ta sauya tunaninsu inda suka samu ilimi da kwarewa a wasu bangarori.
Ya ce bukatar hada kai kan kula da iyakoki da tsaro na da muhimmanci.