Gamayyar Kungiyar Ci gaban Kasuwar Singa da ke Kano a karkashin Jagorancin Shugaban ƙungiyar, Barista Junaidu Muhammad Zakari da Shugaban Dattijan Ƙungiyar kuma shugaban rukunonin Kamfanin Sambajo, Alhaji Salisu Sambajo, sun karɓi baƙuncin tawagar wakilan Jami’ar Skyline da ke Kano a ranar Alhamis 16, ga watan Janairun 2025 a ofishin Sambajo da ke Kasuwar Singa Kano.
Tawagar wakilan Jami’ar Skyline ta kawo ne ziyarar ne a ƙarƙashin jagorancin uban Jami’ar, Mista Nitin Anand da Daraktan Jami’ar, Abubakar Sadik Isma’il.
- Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Donald Trump
- Za A Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano Cikin Watanni 14 – Gwamnati
Babbban makasudin kawo shi ne sanya albarka daga Shugaban Dattijan Kungiyar SIMDA, Alhaji Salisu Sambajo da ƙulla alaƙa mai ƙarfi da ƙungiyar SIMDA kan bunkasa harkokin kasuwanci da ilimi a jihar Kano.
A jawabin Mista Anand na Jami’ar Skyline ya ce, su na neman tabarrakin Alhaji Salisu Sambajo da ƙungiyar SIMDA da kuma neman ta su gudunmawar wajen bunkasa harkokin Jami’ar da ɓangaren ilimi da kasuwanci a Kano.
Ya kuma yi alkawarin bai wa shugabancin ƙungiyar SIMDA ragin kuɗaɗen shiga makarantar da kashi 50 cikin kashi 100 kan duk ɗalibin da Kungiyar ta dauki nauyin bai wa tallafin karatu a jami’ar, sannan Jami’ar za ta bai wa mambobin Kasuwar Singa bita da horo na yini guda kyauta da kuma ba su takardar shaidar horo a kan kasuwancin zamani a matsayin wani bangare na tukuici ga ƙungiyar ta SIMDA.
A jawabin dattijon Ƙungiyar SIMDA kuma shugaban rukunonin Kamfanin Sambajo, Alhaji Salisu Sambajo, ya bayyana farin cikinsa da jin daɗi kan kawo ziyarar wakilan Jami’ar, ya kuma yi alƙawarin bayar da duk wata gudunmowa da za ta kyautata alaƙa kan ci gaban ilimi da kasuwanci a tsakanin ƙungiyar SIMDA da Jami’ar.
Shugaban Ƙungiyar, Barista Junaidu Muhammad Zakari, ya gode wa wakilan Jami’ar bisa karrama su da su ka yi wajen kawo ziyarar, ya kuma ce su ma za su kai musu makamanciyar ziyarar don kara karfafa zumunci da tattaunawa kan yadda za a bunƙasa ɓangaren ilimi da kasuwanci a kasuwar.
Barista Junaidu ya ce, za su duba hanyoyin da za su bi don bayar da ta su gudunmawar a ƙungiyance.
Shugaban ya kuma gode wa Jami’ar kan horo da bitar da Jami’ar za ta shirya wa mambobin ƙungiyar na kasuwar Singa.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin shugabanin ƙungiyar da mambobinta da sauransu.