Sin Ba Ta Taba Kafawa Kasashen Afirka Tarkon Bashi Ba

Daga CRI Hausa,

Da safiyar yau Juma’a 26 ga wata ne, ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya shirya taron manema labarai, domin fayyace abubuwan dake kunshe cikin takardan nan ta bayani, wadda gwamnatin Sin ta fitar, mai fashin baki game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a sabon zamani.

Yayin da yake amsa tambayar da wani dan jarida ya gabatar masa, mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar Sin Wu JiangHao, ya ce zargin da wasu sassa ke yi, cewa wai Sin na kafawa kasashen Afirka tarkon bashi, ba shi da wani tushe ko makama.

Wu JiangHao ya ce akwai matsala game da yadda ake cusa zargi cikin batun ba da bashi ga kasashen Afirka. Alal misali, ta yaya za a kira bashin da kasashen yamma ke samarwa kasashe masu tasowa da bashin raya kasashen, a kuma rika na Sin da tarkon bashi? Yin hakan ba shi da wata ma’ana.

Jami’in ya kara da cewa, “Kamata ya yi mu maida hankali ga yadda kasashen da batun ya shafa ke kallon al’amarin. Ya zuwa yanzu, ban sani ba ko kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun samu wata kasa mai tasowa da ta yi kukan cewa, Sin ta kafa mata tarkon bashi. Ba a taba samu ba. Don haka dai, batun dana tarkon bashi, wasu gwamnatocin kasashen yamma, da ‘yan jaridun su ne suka kitsa shi”.

A nasa tsokaci, daraktan sashen Afirka a ma’aikatar harkokin wajen Sin Wu Peng, ya ce abun da za a iya fahimta daga kalmar tarkon bashi shi ne, tana amfani da karfin tuwo wajen karbe wasu kayayyakin raya kasa dake kasashen Afirka, idan kasashen suka gaza biyan bashin da Sin din ke bin su. Amma a hakika ba wata kasa a Afirka da ta fuskanci wani abu makamancin wannan daga kasar Sin. Don haka dai, shaidu na zahiri sun karyata wannan batu na tarkon bashi, da wasu sassan yammacin duniya ke yayatawa. (Saminu)

 

Exit mobile version