CRI Hausa" />

Sin Da Afrika Sun Hada Kansu Don Yakar COVID-19

A kwanan baya, wani bidiyon raba fasahar yakar COVID-19 da aka gabatar a shafin yanar gizo na sada zumunci na kasar Angola, ya samu karbuwa sosai. Dalibin Angola dake karatu a jami’ar Xiamen ta kasar Sin ne ya dauki wannan bidiyo, don gabatar da matakan da ya gani a kasar Sin, game da kandagarkin cutar, ta wannan hanya yana fatan raba ilimi, da fasahohin yaki, da ma kandagarkin yaduwar cutar ga jama’ar Angola.

Shugaban kasar Angola João Manuel Gonçalves Lourenço ya kalli bidiyon, ya kuma yaba tare da yin kira ga jama’ar kasar, da su koyi abubuwa daga kasar Sin, a fannin yaki da kandagarkin cutar, da kuma ruhin Sinawa na sarrafa kansa don magance cutar tare.
Ban da wannan kuma, an ba da labarin cewa, daga karfe 1 na sanyin safiyar ranar 30 ga watan Maris bisa agogon kasar Ghana, kasar ta dauki matakin takaita fitowa na makwanni biyu a lardin Greater Accara, da birnin Kumasi da karkararsa.
A daya hannun kuma, kamfanonin kasar Sin kuma sun baiwa hukumar kiwon lafiyar Ghana, da asibitin lardin Great Accara, da dai sauran hukumomin dake aikin yakar cutar na’urorin taro a kan Intanet guda 4.
Ministan kiwon lafiya na kasar Kwaku Agyemang-Manu, ya yaba ci gaban da kasashen biyu ke samu wajen hadin kansu, tare da godewa taimakon da kamfanonin kasar Sin suke bayarwa. A cewarsa, dabaru da kuma fasahohin gwamnatin kasar Sin, na yakar cutar na ba da jagoranci matuka ga aikin da aka yi cikin kasarsa, kuma Ghana za ta kara hadin kanta da kasar Sin, da ma duk fadin duniya don yakar cutar tare.
Sannan, mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Kwesi Quartey ya kuma yabawa matakan da kasar Sin ke dauka da kuma kokarin da take yi wajen yaki da annobar cutar COVID-19, kana da yadda kasar ke ci gaba da tallafawa Afrika a yaki da annobar.
Ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da jakadan kasar Sin a AU, Liu Yuxi, wanda ya gudana a helkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a jiya Alhamis.
A wata sanarwar da Quartey ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce, sun tattauna ne game da yadda za’a kara yin hadin gwiwa da zurfafa cudanya tsakanin kungiyar AU da kasar Sin wajen yakar annobar COVID-19 a Afrika.
Taron bangarorin biyu yana daga cikin kokarin da hukumar gudanarwar AU take yi da nufin dakile annobar ta COVID-19, da nufin zurfafa hadin gwiwa tsakanin AU da kasar Sin don kawar da cutar COVID-19 a Afrika, karkashin dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Mai Fassarawa: Amina Xu, Ahmad Fagam)

Exit mobile version