Ga duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum dake gudana a matakin kasa da kasa, ya kwana da sanin cewa, kasar Sin ta sake samun gurbi a hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, sakamakon zabenta da aka sake yi, yayin taron koli na MDD da ya gudana a ’yan kwanakin baya, kuma bisa hakan, za ta kasance cikin mambobin hukumar tun daga shekarar 2024 dake tafe har zuwa 2026.
Wannan ne karo na shida, da Sin din ke samun damar ba da gudummawa a wannan hukuma ta MDD, tun bayan kafuwarta a shekarar 2006. To ko mene ne ya sanya har yanzu ake damawa da kasar Sin a wannan hukuma mai muhimmanci?
- Sin Ta Kadu Ta Yi Tir Da Kisan Jama’a Masu Tarin Yawa Sakamakon Hari Kan Asibiti A Gaza
- Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Zamanintar Da Kasashen Duniya Cikin Shekaru 10 Masu Zuwa
Hakika dalilan suna da yawa, amma kadan daga cikinsu su ne gamsuwar da sassan kasa da kasa suka yi, da irin nasarorin da Sin din ta cimma a bangarorin kare hakkokin bil adama a cikin gida, da ma yadda take taka rawar gani wajen shiga hadin gwiwar kare hakkin bil adama a matakin kasa da kasa.
Sanin kowa ne cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe mambobin farko na MDD, kuma mai kujerar dindindin a majalissar, har kullum kasar Sin na shiga dukkanin ayyukan da suka shafi kare hakkin bil adama, tana sauke nauyin tallafawa ayyukan da suka shafi hakan, kana tana goya baya ga tsarin jagoranci na kare hakkokin bil adama yadda ya kamata.
Har ila yau, duniya ta gamsu da yadda Sin din ke ingiza duk wasu matakai na samun ci gaban manufofin kare hakkin bil adama cikin lumana kuma a dukkanin matakai.
Kaza lika, Sin na martaba ka’idojin MDD, da sauran kudurorin da sassan kasa da kasa suka amince da su game da kare hakkin bil adama, wanda hakan ya sanya ta zama abun koyi ga sauran sassan duniya a wannan fage.
A ganin kasar Sin, kare martabar al’umma shi ne babban jigo na tabbatar da hakkokin bil adama, wato dai farin cikin al’umma shi ne kan gaba, idan ana batun kare hakkin bil Adama.
Ko shakka babu, al’ummar kasar Sin na kara cin gajiya daga nasarorin kasarsu, kuma Sin na sanya bukatun jama’a gaban komai, tana goyon bayan duk wasu tsare-tsare na samar da ci gaban al’umma daga dukkanin fannoni, ta yadda duniya ke yabawa, da irin gudummawarta a bangaren kare hakkokin bil Adama. (Saminu Alhassan)