Daga CRI Hausa,
A yau Litinin kasar Sin ta tura kumbon daukar kaya na Tianzhou-3 domin jigilar wasu kayayyaki zuwa tashar sararin samaniya da take aikin ginawa.
Kumbon Long March-7 Y4, mai dauke da kumbon Tianzhou-3, ya tashi daga tashar harba tauraron dan Adam ta Wenchang dake lardin Hainan, kamar yadda hukumar kula da ayyukan sararin samaniyar kasar Sin (CMSA) ta bayyana.
A cewar hukumar ta CMSA, daga bisani kumbon Tianzhou-3 zai hadu da muhimmin rukunin Tianhe da kumbon Tianzhou-2 a tashar sararin samaniyar.