Yau 24 ga watan Satumba, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai bisa taken “fara aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar karo na 15”.
A taron, wani jami’i mai kula da harkokin al’adu da yawon bude ido ya bayyana cewa, Sin ta zama kasa mafi yawan mutane da ake zuwa shakatawa daga kasashen waje da kuma babbar kasa mai karbar bakin yawon bude ido daga kasashen duniya.
A shekarar 2025, adadin masu shigowa kasar don yawon bude ido ya kai miliyan 154, wanda ya karu da kashi 17.1% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata, adadin mazauna cikin kasar da suka tafi kasashen waje don yawon bude ido ya kai miliyan 148, wanda ya karu da kashi 20.8 % idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
A cewar bayanin, ci gaban harkokin yawon bude ido na Sin na dogaro da mabambantan albarkatu, kamar bambancin yanayin halitta da tarihi da al’adu. Bugu da kari, Sin ta gina tsarin hanyoyin jirgin kasa mai sauri mafi girma a duniya, da tsarin hanyoyin mota, kuma cibiyar sadarwar wayar hannu ta isa karkara da birane, wanda hakan ya tabbatar da karfin Sin a fannin ababen more rayuwa na yawon bude ido.(Amina Xu)














