A yau Litinin aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na bana, inda Xi Jinping, wanda aka sake zabarsa a matsayin shugaban kasar Sin a wajen taron, ya yi jawabi don bayyana ayyukan da za a mai da hankali a kansu cikin sabon wa’adin aikinsa. A cewarsa, kasar Sin za ta yi kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, da samar da karin gudunmowa don tabbatar da zaman lafiya a duniya, da ci gaban kasashe daban daban.
Duk burikan da kasar Sin ta sanya a gaba suna da girma. Sai dai ta yaya kasar za ta iya cika su kamar yadda ta tsara?
Za mu iya duba matakan da kasar ta dauka a baya a wadannan fannoni.
Aikin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama ya shafi yunkurin tabbatar da ci gaban kasashe daban daban na bai daya. A wannan fanni, kasar Sin ta dade tana taimakawa kasashe masu tasowa wajen raya tattalin arziki, da gina kayayyakin more rayuwa, gami da kyautata zaman rayuwar al’ummominsu.
Idan mun dauki dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a matsayin misali. Tun bayan da aka kafa dandalin a shekarar 2000, har zuwa yanzu, kamfanonin kasar Sin sun taimakawa kasashen Afirka a fannonin gina da inganta layin dogo da tsayinsu ya zarce kilomita dubu 10, da hanyoyin mota da tsawonsu ya kai kusan kilomita dubu 100, da gadojin da yawansu ya kusan kai dubu 1, da tashohin jiragen ruwa kusan dari 1, gami da dimbin asibitoci da makarantu, inda aka samar da sabbin guraben aikin yi fiye da miliyan 4.5 ga mazauna wuraren da batun ya shafa.
Ban da wannan kuma, zaman lafiya da kwanciyar hankali,shi ne tushen ci gaban tattalin arziki. Ganin haka ya sa sojojin kasar Sin suka kwashe dimbin shekaru suna kokarin wanzar da zaman lafiya a wasu kasashen dake nahiyar Afirka da suka hada da Mali, da Sudan ta Kudu, da dai sauransu, da ba da kariya ga jiragen ruwan dakon kayayyakin ciniki da suke bi ta mashigin teku na Aden, da yankin tekun dake dab da kasar Somaliya, da samar da tallafin likitanci, da kai dauki na gaggawa, ga kasashen da suke da bukata, da dai makamantansu.
Haka zalika, a kwanan baya, bisa shiga tsakani da kasar Sin ta yi, kasashen Saudiya da Iran sun yanke shawarar kawo karshen kiyayya da juna, da maido da huldar diplomasiyya tsakaninsu, lamarin da ya aza harsashi ga kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. Inda kasar Sin maras nuna son kai, wadda ta ki karkata ga wani bangare, ko kuma kulla wani rukuni, ta cimma nasarar yin sulhu, da kasashen yamma suka gaza neman ganin hakan ya tabbata, ta hanyar tsara manyan tsare-tsare bisa ra’ayin kai, da yin shawarwari don daidaita matsaloli.
Ta haka muna iya ganin cewa, kasar Sin ta dade tana kokarin aiwatar da matakai daya bayan daya, don taimakawa daidaita al’amura a duniyarmu.
Sai dai mene ne ra’ayoyin sauran kasashe dangane da ayyukan da kasar Sin ta yi, da muka ambata a sama?
Don amsa wannan tambaya, za mu iya duba sakonnin da wasu shugabannin kasashen Afirka suka aikewa shugaba Xi Jinping don taya shi murnar samun karin wa’adin shugabancin kasar. Inda Wavel Ramkalawan, shugaban kasar Seychelles, ya ce, “Kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kokarin sake gina wani tsarin duniya mai tushen girmama ra’ayoyin bangarori daban daban, da daukaka zaman lafiya, da hadin kai.” A nasa bangare, shugaban kasar Eritrea, Isaias Afwerki, ya ce yana da imani kan cewar “kasar Sin za ta samar da muhimmiyar gudunmowa ga kokarin gina wani nagartaccen tsarin kasa da kasa da zai amfani bangarori daban daban”. Kana Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan, shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Sudan, ya ce “ Kasar Sin za ta hada kai da abokanta a kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasashe daban daban a duniya, da gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya tare.”
Sai dai maganar da ta fi burge ni, ita ce wadda Patrice Guillaume Athanase Talon, shugaban kasar Benin, ya fada, yayin da yake hira da wakilin wani gidan telabijin na kasar Faransa a kwanan baya. Inda ko da yake an yi kokarin juya amsarsa, amma duk da haka, shugaban ya tsaya kan nuna yabo ga kasar ta Sin. A cewarsa, “kasar Sin ta kasance kasar da ba wanda zai iya kyale ta a duniya. Kana kasar tana ba ni kwarin gwiwa. A ganina, tsari na raya kasa na kasar Sin, da yadda take dogaro da kanta, da nagartacciyar dabararta a fannin mulki, za su karfafa gwiwar dukkan kasashen da suke fama da koma bayan tattalin arziki, saboda misalin kasar ta nuna cewa, duk wata kasa za ta iya samun ci gaban tattalin arziki.”
Rawar da kasar Sin ta dade tana takawa a duniya ita ce, kokarin wanzar da zaman lafiya, da neman ganin ci gaban kasashe daban daban, da hadin gwiwa da su don tabbatar da moriyar juna, gami da kokarin raya kanta, ta yadda za ta iya samar da fasahohi masu amfani ga sauran kasashe, da karfafa gwiwarsu, a kokarin da suke na neman samun ci gaba. Kuma kasar za ta ci gaba da kokarin taka wannan muhimmiyar rawa a nan gaba. (Bello Wang)