‘Yan’uwana mata da sauran masu karatu da ke biye da mu a wannan shafi naku mai farin jini na Ado Da Kwalliya ina yi mana barka da sake saduwa a wannan makon.
A yau shafin namu ya yo muku tsaraba ne da wani sirri da ke tattara da abarba wajen gyaran fata.
Za ku yi mamakin babbar fa’idar da ake samu daga abarba, baya ga fa’idojin da take da su a bangaren inganta lafiyar jiki kamar shahararren sirrinta na narkar da abinci da kuma habaka rigakafi. Abarba tana da matukar kyau da tasiri wajen inganta lafiyar jama’a gaba daya, amma baya ga haka abin da wannan kayan marmarin yake yi na musamman da yake da matukar mamaki shi ne abin da za mu zo da shi a rubutun namu na yau wanda yake da matukar kyau da amfani.
Wannan ‘ya’yan itace yana da isasshen sinadarin Bitamin da sinadarin kara karfin kashi da sauran sinadarai irin su ‘manganese’, ‘calcium’, ‘sodium’, da magnesium, wadannan duk suna cikin abarba.
Binciken masana kiwon lafiya da masana bangaren magungunan da abinci ke yi ga dan’adam sun tabbatar da cewa abarba tana habaka lafyar fata idan aka sha ta yadda take ko ta hanyar shafa ruwanta a-kai-a-kai.
Ga sauran wasu sirrukan abin da abarba ke yi ga dan’adam:
1.Yaki da Tsufa: Akwai mutane da dama wadanda suke da shekaru a duniya amma sun tsani a rika yi musu kallon tsufa.
To ina ire-iren wadannan?
Hanya mafi sauki da za ku rika yakar tsufanku ita ce ku rika shan abarba a-kai-a-kai. Lallai bincike ya tabbatar da abarba tana jinkirta saurin tsarin tsufa saboda sinadaran da take dauke da su na yaki da tamushewar fata.
2.Tana rage duhu ko tabon baki a jiki
Abarba tana dauke da wadatacciyar sindarin ‘ascorbric acid’ wadda yake matukar taimakawa wajen yaki da tabon ciwo da ya yi baki a jiki. Haka nan idan kina son kawar da bakin da ba ki so a wata gaba ta jikinki, kawai ki shafa ruwan abarba a kan wuraren da suke da duhun, ki barshi na tsawon mintuna biyar, sannan ki wanke da ruwan dumi, za ki sha mamaki cikin yardar Allah.
3. Barkewar kurajen fuska. Har ila yau, wani sirri da abarba take dauke da shi shi ne kawar da kuraje masu sa duhu a fuska, ana ba da shawarar cewa idan mace tana son hana wadannan kurajen na fuska su bata mata kyawon fuska ta rika shafa yankan abarba za ta samu waraka.
4. Gyara fata
Abarba tana kunshi da sinadaran ‘enzymes’ wanda ke cire matattun kwayoyin halittar fata da kuma haskaka fata. Don haka, idan kina so fatarki ta kara haske (ba irin na bilicin ba), ki rungumi sha da shafa abarba.
5.Tana taimaka wa warkar da raunuka
Abarba tana da sinadarin maganin ‘antiodidant’, da na Bitamin C, wadanda suke iya taimaka wa wajen hana lalacewar kwayoyin fata, don haka idan aka yi amfani da ita tana iya taimakawa wajen saurin warkar da rauni ta hanyar tallafa wa samar da sabbin kwayoyin fata.
Ina fata mun amfana da wannan tsaraba. Sai kuma mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.