Shalƙwatar tsaron ƙasa ta bayyana cewa dakarun Soji da ke gudanar da ayyuka na cikin gida sun kama ‘yan ta’adda 1,191 ciki har da manyan shugabanni, tare da ceto mutane 543 da aka sace cikin watanni uku daga Afrilu zuwa Yuni 2025.
Babban Daraktan Harkokin Yaɗa Labaran rundunar, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani ga manema labarai game da ayyukan rundunonin tsaro a rabin shekarar 2025.
- Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS
- Matatar Dangote Za Ta Fara Dakon Man Fetur Da Dizal Kyauta A Fadin Nijeriya
Manjo Janar Kangye ya ce dakarun Sojin sun hallaka manyan shugabannin ‘yan ta’adda kamar su Amir Abu Fatimah, Kinging Auta, Abdul Jamilu, Salisu, Mallam Jidda, Maiwada, Mai Dada da Nwachi Eze da aka fi sani da Onowu. Ya ƙara da cewa mutum 682 daga cikin ‘yan ta’adda da iyalansu sun mika wuya ga Sojoji kawo wannan lokaci.
A cewar Kangye, kwana biyu da suka wuce, wani babban shugaban ‘yan fashi mai suna Yellow Danbokkolo ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a musayar wuta da Sojoji, inda wasu daga cikin kwamandojinsa ma aka kashe su.
Ya bayyana cewa wasu da ake zargi da safarar makamai da garkuwa da mutane da suke cikin jerin sunayen waɗanda Sojojin ke nema sun shiga hannu kuma ana gudanar da bincike a kansu.
A wani ɓangaren kuma, rundunar Operation DELTA SAFE ta bankaɗo da kuma karɓo danyen mai da aka sace wanda ya kai darajar Naira biliyan 3.5. Haka kuma, an karɓo lita 2,381,239 na ɗanyen mai, lita 605,393 na man diesel da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, lita 41,465 na man fetur DPK da kuma lita 26,905 na Fetur. Rundunar ta lalata haramtattun wuraren tace man 174, tare da kwace motoci 45 da makamai da nakiya iri-iri da aka shirya domin tayar da su.














