Rundunar sojojin kasan Nijeriya, ta tabbatar da sake buÉ—e rukunin shagunan kasuwanci na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja bayan rufe su da aka yi sakamakon wani rikici da ya faru a watan Afrilu.
Ranar Lahadi ne kuma 19 ga wata, rundunar sojin ta rufe wajen ne domin gudanar da bincike kan ayyukan da ta bayyana a matsayin na masu aikata barna.
- Ranar Yara Ta Duniya: Inganta Rayuwar Yaran Nijeriya Shi Ne Abu Mafi Girma – Tinubu
- Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Ƙananan Hukumomin Zamfara
Kafin rufewar wani bidiyo ya karade shafukan yanar gizo inda wasu mutane suka far wa wasu sojoji a kusa da rukunin shagunan.
Bidiyon ya nuna yadda wasu ‘yansanda suka shiga tsakani domin ceton jami’an sojin da mutanen suka yi wa dukan tsiya.
Darektan hulda da jama’a na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce matakin sake budewar na daga cikin matsayar da aka cimma a taron da aka yi a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, da shugabannin rukunin shagunan da sauran shugabannin hukumomin tsaro na Abuja.
Janar Onyema, ya ce daga cikin matakan da aka dauka a taron har da rufe shago mai lamba C93, da kuma kama masu shagon da aka yi rikicin.