ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Sojojin Sama

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ta sanar da cewa ɓangaren Sojojin sama na Operation Whirl Stroke sun kai hare-hare ta sama wanda ya hallaka ‘yan ta’adda da dama a maɓoyarsu da ke ƙananan Hukumomin Giwa da Igabi na Jihar Kaduna.

A cewar wata sanarwa da AVM Edward Gabkwet, Daraktan hulɗa da Jama’a ya fitar, ana ci gaba da samun nasara a waɗannan hare-haren duk da matsalolin yanayi da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.

  • Mutane 20 Sun Mutu, 52 Sun Ji Rauni A Harin Bam A Borno – DHQ
  • Sabbin Hare-haren Kunar Bakin Wake A Borno Jama’a Na Fargabar Jiya Ta Dawo Yau

Ɗaya daga cikin hare-haren da aka kai shi ne a ranar Juma’a a maɓoyar Alhaji Layi dake ƙauyen Kufan Shantu, ƙaramar hukumar Giwa, inda aka lalata kayan aiki da ‘yan ta’addan suka ɓoya a ƙarƙashin bishiyoyi.

ADVERTISEMENT

An samu nasarar kai wani hari a ranar Asabar a sansanin ‘yan ta’adda a cikin dajin Malum da ke ƙaramar hukumar Igabi. Harin dai an kai shi ne bayan samun cikakkun kwararan bayanan sirri, tare da gudanar da lissafi da leken asiri, ya kashe mafi yawan ‘yan ta’addan da aka gani suna yawo a cikin dajin.

Waɗannan hare-haren ta sama an yi su ne sakamakon bayanan sirri da suka nuna wuraren da aka nufa a matsayin maboyar ‘yan ta’addan da suka kai hari kan sojoji a Manini a ranar 10 ga Yuli.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa

Sojoji Sun Kama Babban Mai Sayar Da Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Ta’adda Na Boko Haram

AVM Gabkwet ya jaddada cewa NAF, tare da haɗin gwuiwar Sojojin ƙasa, za su ci gaba da samun rinjaye ta hanyar lura da yanayi, da gudanar da sintiri akai-akai, da kuma kai hare-hare kai tsaye kan maɓoyar ‘yan ta’adda. Wannan dabarar na nufin kawar da ta’addanci da sauran laifuka a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Tsaro

‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa

November 29, 2025
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
Tsaro

Sojoji Sun Kama Babban Mai Sayar Da Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Ta’adda Na Boko Haram

November 21, 2025
NDLEA
Tsaro

NDLEA Ta Kama Ƙwayar Tiramadol 396,000 A Filin Jirgin Saman Yola

November 21, 2025
Next Post
Sufeta Janar Na Ƙasa Ya Dakatar Da Aiwatar Da Na’urar E-CMR Bayan Shan Suka

Sufeta Janar Na Ƙasa Ya Dakatar Da Aiwatar Da Na'urar E-CMR Bayan Shan Suka

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.