Connect with us

LABARAI

Su Waye Ke Neman Ganin Bayan Baffa Babba A Shugabancin Karota?

Published

on

Tun bayan wani bayani da Manajan darakta na hukumar kulada cunkoson ababen hawa na jahar Kano da akafi sani da KAROTA Dokta Baffa Babba dan’agundi ya yi na dalilan janyewar jami’ansu daga kan hanyoyin jihar Kano a kwanakin baya da cewa saboda samun rade-tadin cewa wasu bata gari na nufin aukawa jami’ansane tasa wasu keta kira ga Gwamnatin Kano akan lallai ta sauke shugaban KAROTA daga mukaminsa.

Masu wadanan kiraye-kiraye ga Gwamnati da suka hada da wasu cikin yan jam’iyyarsa ta APC harma da wasu daga yan karamar hukumarsa ta Birni da kewaye da yan hamayya daga wasu jam’iyyu da wasu kungiyoyin al’umma sun danganta kalaman na Baffa Babba da cewa barazanace ga tsaro da bai kamata ace anji irinta daga bakin ba domin hurumine na jami’an tsaron yan sanda.

Sunce kalaman nasa kan iya sanya fargaba da razani a tsakanin al’umma dan haka sukeda bukatar Gwamnatin Kano ta cire shi daga matsayin shugaban na KAROTA.

Aminu Adam Gwale daya daga masu irin wannan kiraye-kiraye yace dama matsayinda aka baiwa Baffa Babba na Manajan Daraktan Hukumar ababen hawan ya sabawa ka’idar dokarda ta Kafa hukumar wanda ta sahale cewa sai babban jami’in tsaro da yayi ritaya ko tsohon jami’i na sashin kulada ababen hawa.”bIO”Sune doka ta baiwa damar damar su shugabanci hukumar amma sai aka karya wannan ka’idar aka baiwa Baffan tun daga bashi aketa samun korafe-korafe marasa dadin ji na karya ka’idar aikin hukumar.

Sai dai wasu na ganin masu nuna hamayya da shugabancinda Baffa Babba yake na KAROTA wasune kawai da yan cikin jam’iyyarsu da sukeyi masa hassada duba da irin nasarori da hukumar ke samu.Daga daya bangaren kuwa hamayyace kawai da Gwamnati tasa masu fadar a cireshi tasa suke fada.

Sai dai tun zamansa shugaban na KAROTA jama’a keta korafi da salon aikinda jami’ansa suke da wani lokacin takan kaiga sun jikkata masu ababen hawa ko yiwa motoci rotse da wasu kulake da hukumar KAROTA ta basu dama suka tsiri rikewa tun zuwan Baffa Babba.

Ko’a kwanakin baya ma saida rundunar yansandan tayi jan hankali ga Manajan Daraktan na KAROTA akan ya rika horarda jami’ansa kan yin kyakkyawar mu’amala da al’umma musamman masu ababen hawa kamar yanda jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan na jahar Kano ASP Kiyawa ya shaidawa manema labarai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: