Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan na gab da zama kasa mafi fama da yunwa sanadin yaki a duniya, bayanin da ke zuwa bayan watanni 11 da fara yakin kasar.
Rikicin da ke tsakanin Jagoran gwamnatin sojin kasar, Abdulfattah AlBurhan da shugaban rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, Mohammed Hamdan Daglo, ya lakume rayukan dubban mutane tare da rusa kasar da kuma durkusar da tattalin arzikinta.
- NiMet Ta Yi Hasashen Bullar Zazzabin Cizon Sauro A Watan Maris Da Afrilu
- An Kama ‘Yan Sintiri 10 Kan Zargin Kashe Limamin Garin Mada
Yakin na watanni 11 ya raba mutane sama da miliyan takwas da muhallansu, abin da ya sanya yakin matsayin wanda ya fi kowanne haddasa hijira a duniya.
Da ta ke jawabi, shugabar hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya, Cindy McCain, ta ce a yanzu yunwa ita ce babbar barazanar da fararen hula a Sudan ke fama da ita.
Shekaru 20 da suka gabata yankin Darfur shi ne mafi fama da tsananin yunwa sanadin yaki a duniya, sai dai yanzu akwai yiwuwar yankin ya yi kunnen-doki da Sudan.
McCain, ta nuna takaicinta kan yadda duniya ta manta da Sudan da irin tsanannin da fararen hular kasar ke ciki duk a sakamakon yakin da za a iya magance shi ta hanyar masalaha.