ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Yaya Kasashe Masu Tasowa Za Su Iya Tinkarar Yakin Haraji Da Amurka Ta Tayar?

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Haraji

A bayyane take dai matakin da Amurka ta dauka na kakaba haraji kan kayayyakin da ake shigar da su Amurka wani salo ne na yakin cinikayya, da nufin karya wasu kasashen da Amurka din take ganin irin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin da suke samu, abin da kuma yake tsonewa Amurka ido.

To sai dai abin da Amurka ta gaza fahimta a nan shi ne, sauran kasashen da wannan mataki ya shafa ba za su rungume hannuwansu su zura mata ido ba ta yi abin da ta ga dama. Babu makawa su ma za su mai da martani. Kasashe masu tasowa da ake kira Global South, wadda China take taka muhimmiyar rawa a ciki , sun yunkuro domin mai da martani ga wannan mataki na haraji da Amurka ta bullo da shi, don tabbatar da adalci tsakanin kasashe. Musamman bisa la’akari da yadda Amurka ke nuna kaka gida tare da karya dokokin kasa da kasa gami da barazanarwa domin biyan bukatun kanta. Duk kuwa tana aikata hakan ne ba tare da la’akari da muradun sauran kasashe ba. Misali, idan Amurka na fakewa da cewa ai akwai kasashen dake shigar da kayayyaki zuwa Amurka fiye da kayayyakin da take fitarwa zuwa irin wadannan kasashe, shi ne dalilinta na fito da wannan tsari na haraji, to amma ta manta da cewa akwai wagege gibin cinikayya tsakaninta da wasu kasashe masu tasowa kamar kasar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, CAR? Wadda daga cikin adadin yawan cinikayyarsu ya kai dala miliyan 36.5, amma adadin kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa Amurka bai fi dala miliyan 1.4 ba, ke nan akwai gibin cinikayya na kimanin dala miliyan 33.6. Ke nan daidaiton cinikayya bai amfani irin wadannan kasashe masu tasowa na Global South ba.

  • Gamayyar kungiyoyin Seyi Tinubu (STSG) Na Shirin Gangamin Taronta Na Kasa
  • Ramuwar Gayya: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Yawa A Borno

Ya kamata mu sani cewa Amurka ta fito da wannan tsari na haraji ne domin ganin ta karya duk wata kasa da ta yunkuro domin bunkasa tattalin arzikinta. Kamar irin abin da ya faru ga kasar Cambodia, wadda ta fara yin fice a fasahar allon hasken rana mai samar da wutar lantarki, kafin Amurka ta zabga mata haraji na fitar hankali. Ba a taba ganin irin wannan kazamin haraji ba a kan duk wani kamfani dake harkar samar da makamashi daga hasken rana. Wannan lamari ya tilastwa Cambodia rufe kamfanoninta tare da sallamar dubban ma’aikata daga bakin aikinsu.

ADVERTISEMENT

Ba shakka, kasashe masu tasowa su ne wannan mataki ya fi yi wa illa, kamar dakile musu ci gaban kimiyya da fasaha gami da bunkasuwar masana’antu. Farautar masu zuba jari daga Afirka da Asiya da Latin Amurka ta hanyar yi musu barazana da haraji ba karamin koma baya zai iya kawo ba a wadannan kasashe ba.

 

LABARAI MASU NASABA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

December 17, 2025
Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Aka Kayyade Yin Amfani Da Sinadaran Narkar Da Kankara A Beijing

December 16, 2025
Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI
Ra'ayi Riga

Waiwaye Adon Tafiya : Tasirin Sin A Kan Afirka Ta Fannin Fasahar AI

December 15, 2025
Next Post
Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai

Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.