Kwararru na ganin cewa, wannan rashin jituwa ta fuskar kasuwanci tsakanin Amurkan da Indiya, zai iya shafar burin da Kasashen biyu suka sa a gaba, na dakile karbuwar da Chana ke kara samu a kasuwannin duniya.
Indiya ta kara kudaden harajin da take karba kan kayayyakin Amurka da ake shiga da su Kasar, yayin da takaddamar cinikayya ke kara zafafa tsakanin Kasashen biyu.
Wannan mataki na martani da Indiyan ta dauka, na zuwa ne kwanaki bayan da hukumomin Washington suka cire Indiyan daga jerin Kasashen da ke da gatan yin cinikayya da Amurka ba tare da wata takura ba. Takaddamar cinikayyar har ila yau na zafafa ne, gabanin wata ziyara da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo zai kai a Kasar.
Amurka na son Indiya ta ba kamfanoninta karin damar yin hada-hada a kasuwanninta, ta kuma rage takunkuman cinikayya. Kwararru na ganin cewa, wannan rashin jituwa ta fuskar kasuwanci tsakanin Amurkan da Indiya, zai iya shafar burin da Kasashen biyu suka sa a gaba, na dakile karbuwar da Chana ke kara samu a kasuwannin duniya.