Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya cika alkawarin tallafawa masu kananan sana’o’i dubu 10, da Naira 50,000 kowanensu, da nufin bunkasa harkokin kasuwancinsu a sassan jihar.
Fintiri, ya bayyana haka a taro da masu kananan sana’o’in a dandalin taro na Mahmud Ribadu da ke Yola, ranar Juma’a.
- Kasar Sin Ta Gano Filin Hakar Mai Na Farko A Ruwa Mai Zurfi Mai Yawan Ton Miliyan 100
- Rikita-rikitar Sauka Da Komawar Sheikh Daurawa Shugabancin Hisbar Jihar Kano
Ya ce shirin na karfafawa da aka yi wa lakabin ‘yan kasuwan Fintiri’ muhimman ci gaba ne a yunkurin gwamnatoci na daukaka martabar zamantakewa da tattalin arzikin al’umma da ya hada duk bangarorin tattalin arziki.
M
Ya ci gaba da cewa “A matsayin gwamnati ta fahimci cewa kananan sana’o’i su ne kashin bayan al’ummomin yanki, da samar da sabbin abubuwa, samar da ayyukan yi, da kuma bayar da gudunmawar ci gaban jama’a da jiha.
“Shawarar raba wadannan kudade ya samo asali ne daga jajircewar da aka nuna na kawar da talauci da kuma bai wa ‘yan kasuwa damar bunkasa a kasuwannin hada-hadar kudade.
“Mun yi amanna ta hanyar bada taimakon kudi kai tsaye ga masu kananan kasuwanci dubu 10, muna da niyyar habaka kudirinsu, habaka ayyukansu, da ba su damar habaka ayyukansu zuwa ga samun ci gaba.
“Na fahimci kalubalen da masu kananan sana’o’i ke fuskanta, kama daga rashin isasshen jari zuwa karancin kayan aiki da ababen more rayuwa, da irin wadannan tallafin kudi ba kawai na hannu ba ne, a’a dabarun saka hannun jari a Jihar Adamawa,” in ji gwamnan.
Da yake magana kan mutanen da suka amfana da shirin, gwamna Umaru Fintiri, ya bukaci da su yi amfani da kudaden yadda ya kamata, ya ce su zuba jari a cikin sana’o’insu, tare da yin amfani da damar da ke gabansu, samar da kirkire-kirkire, kere-kere, da ya ce nasarar da su ka samu na da nasaba da ci gaban jihar.
Shi ma da yake jawabi, kwamishinan ma’aikatar bunkasa harkokin kasuwanci ta jihar, Honarabul James Iliya, ya ce shirin ‘yan kasuwan Fintiri ya taba duk wani lungu da sako na al’ummar jihar, ya yaba wa gwamnan bisa cika alkawarin da ya yi a yakin neman zabe.
Tun da farko da take jawabi shugabar hukumar PAWECA, Hajiya Aisha Bawa Bello, ta bayyana wadanda suka ci gajiyar shirin a matsayin ‘yan kasuwa, ta kuma yaba wa gwamnan bisa irin damar da ya ba su, da ba kasafai ake samu ba na yi wa al’umma hidima.
Ta ce an zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin dubu 10 ne daga sassa 226 na jihar, ta kuma bayyana wasu nasarorin da gwamnan ya samu tare da yin kira ga wadanda suka amfana da su mayar da hankali wajen sanin ya kamata da aiki tukuru.
Da ta ke magana a madadin wadanda su ka ci gajiyar shirin, Eunice Kiliyobas ta bayyana gwamna Fintiri a matsayin wanda ya kuduri aniyar bai wa mabukata dama, ta ce za su yi amfani da tallafin bisa hanyar da ta dace.