Reshen jam’iyyar NDC na Jihar Kano ya danganta rashin bayyanar sunan ɗan takararta na gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, a jerin sunayen ’yan takarar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa, kan tangarɗar na’ura.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Hussaini Isah Mairiga, ya ce za a ɗora sunayen ’yan takarar biyu a ranar Talata, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa za a warware matsalar.
Mairiga, wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawar wayar tarho da jaridar LEADERSHIP, ya jaddada cewa Gwarzo da Kwankwaso har yanzu su ne ɗan takarar gwamna da mataimakinsa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Ya ce ya tuntuɓi jami’an jam’iyyar da ke da alhakin ɗora sunayen ’yan takara, kuma yana tattaunawa da jami’an INEC da ke hedikwatar hukumar a Abuja domin magance matsalar.
Shugaban na NDC ya ƙara da cewa matsalar ba ta shafi Jihar Kano kaɗai ba, yana mai cewa wasu ’yan takarar jam’iyyar a wasu jihohin ma sun fuskanci irin wannan matsala.














