Umar A Hunkuyi" />

Tankar Mai  Ta Kone Mutum 9 Da Mota 54 A Legas

Mutane da yawa ne suka mutu, sa’ilin kuma da mota 54 suka kone kurmus a shekaran jiya, sakamakon faduwa da kamawar da wata motar tankar mai ta yi da wuta a kan babban titin Legas zuwa Ibadan a Jiya.

Hadarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin shekaran jiya a daidai gadar Otedola da ke kan babban titin, motar da ke barin garin na Legas shake da man fetur, ta kwacewa direban motar ne inda nan take motar tankar ta fadi, ta kuma yi bindiga da dukkanin lita 33,000, na man da ke cikinta.

Inda nan take kuma wuta ta kama tankar man, da ma sauran motocin da ke kusa. Mutane da yawa da ke cikin motocin wutan duk ta kama su, sa’ilin da wasu su suka sami tsira da kyar.

A cewar hukumar kare hadurra ta kasa, abin ya shafi ita motar tankar ce kanta, motocin bas-bas guda biyar, manyan motoci biyu, keke napep guda da kuma wasu kananan motocin guda 45.

Hukumar kare hadurran ta tabbatar da mutuwar mutane 9, hudu kuma sun sami munanan raunukana kuna, kamar yadda kwamandan shiyya na hukumar, Mista Hyginus Omeje, ya shaida mana, inda ya kara da cewa, yawan mamatan ma yana iya fin hakan.

Sai dai, wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce, yawan wadanda suka rasu a hadarin zai iya kai wajen 20, masu raunuka kuma za su iya kai wa 50. Emeka Ogwu, wanda yana kan hanyarsa ta koma wa gida ne hadarin ya faru.Ya kara da cewa, lokacin da hadarin ya faru, mutane sun yi ta gudu ta ko’ina, amma wasu sun kasa fitowa daga cikin motocin nasu ne kasantuwar suna daure ne da belt dinsu a cikin motocin nasu, wasu kuma sun kasa bude kofar motocin nasu ne su fito.

Hadarin dai ya haddasa cunkoso mai tsanani a kan hanyar ta fita da kuma shiga garin na Legas.

Gwamnatin ta Jihar Legas, ta taya iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su jimami kan aukuwar hadarin.

Sanarwar gwamnatin Jihar wacce Kwamishinan yada labarai na Jihar, Kehinde Bamigbetan, ya sanya wa hannu, ta bayyana aukuwar hadarin a matsayin wani babban abin bakin ciki da takaici.

Sanarwar na cewa, “A madadin gwamnatin Jihar Legas, muna taya iyalan wadanda wannan mummunar hadarin ya rutsa da su jimami da bakin cikin aukuwar hakan. Muna kuma yin addu’a a tare da suna Allah Yaji kansu.

Kwamishinan ya ce, Gwamna Ambode, ya umurci dukkanin hukumomin  da lamarin ya shafa da su hanzarta isa wajen da hadarin ya auku domin su bayar da dukkanin taimakon da ya dace.

 

Exit mobile version