A shekarar 1968 ne, aka nada Alhaji Isa Kaita, shugaban Hukumar daukar ma’aikata ta Jihar Arewa ta tsakiya a zamanin Gwamnan Jihar Birgediya Abba Kyari ne, bugu da kari ya rike mukamin har zuwa watan Agusta na shekarar 1975. Daga 1 shekarar 1975 zuwa1977, Alhaji Isa Kaita, shi ne shugaban Hukumar Gidaje ta Jihar Kaduna. Ya yi tafiye- tafiyen aiki zuwa kusan dukkan kasashen Afrika, Turai, Amurka, Australiya, Asiya, da kuma New Zealand. Ya yo wakilci a Hukumar Alhazai ta kasa, a matsayin wakilin majalisar koli ta kula da harkokin Addinin Musulunci daga watan Agusta na shekarar 1978 zuwa watan Mayu na 1981. Har ila yau shi ne ma’ajin majalisar koli ta harkokin Addinin Musulunci daga shekarar 1977, har zuwa lokacin da ya rasu.
Ya kuma rike mukamai da dama da suka hada da-:
Ya zama mai bada shawara ga Bankin UBA na Nijeriya daga 1972 zuwa1972.
Ya zama Darekta na Bankin Indiya, wanda daga baya kuma sai Allied Bank dag shekarar 1972-1972. Ya zama Darektan Bankin Union Dominion daga shekarar 1972 zuwa1975 ,Ya yi Darektan Kamfanin U. A. C.
Darekta na kamfanin Kayce Challrams, Safa Foam Abbot, Songhai, Kuma shi ne shugaban Hukumar harshen Hausa tun daga shekarar1 960.
Alhaji Isa Kaita, mutum ne mai kaunar karance-karance, da wasanni. A sha’anin wasanni, shi ne shugaban kulob din kwallon kafa na Dawaki na Kaduna tun daga 1960 zuwa har lokacn da ya bar duniya, shi ne shugaban kulob na Sukuwar Dawaki ta Kaduna tun daga 1958, har zuwa shekarar da ya rasu, shi ne Uban kulob din da ake kira da suna Crocodile daga 1970, har zuwa lokacin daya rasu, ya zama wakili a Rotary club na Kaduna. Yana dda cikin iyayen kungiyar wasan fibes na Kaduna da aka nada a shekarar 1968.
A shekarar 1980 ce tsohon Shugaban kasar Nijeriya, Alhaji She Usman Aliyu Shagari, ya nada shi shugaban Hukumar kula da da’ar ma’aikata, majalisar dattijai haka ta amince da nadin na sa. A ranar 16 ga watan Yuli na shekarar1981 ne Shugaban kasa ya rantsar da shi kan shi mukamin. Bayan juyin mulkin na ranar 31 ga watan Disamba na 1983 ne, Alhaji Isa Kaita ya koma Kaduna a watan janairu na 1984, bayan da aka rushe Hukumar kula da da’ar ma’aikatan ranar 5 ga Janairu 1984. Allah ya kawo karshen rayuwar Alhaji Isa Kaita ranar 26 ga watan Nuwamba 1994, bayan da ya yi fama da jinyai muna addu’ar Allah ya jikansa da kuma Rahamsheshi.
Wannan shi ne karshen tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina mako mai zuwa da yardar Allah za mu kawo maku wani tarihi.














