ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Makarantar Katsina-kwalej Zuwa Ta Horon Malamai (1)

by Rabi'u Ali Indabawa
7 months ago
Katsina

Kwalejin horon Malaman makaranta ko Katsina Kwalej ta Katsina ita ce tsohuwar makaranta a Arewacin Nijeriya wadda aka gina ta. a shekarar 1921 dalibai suka fara karatu a cikinta 1922.

An gina tane da tubulin kasa ne wanda aka kona.Halin da ake ciki yanzu ta zama wurin ziyara ind masu yawo shakatawa suke zuwa su kashe kwarkwatar ido duk lokacin da suka zo Katsina.An maida wurin inda ya kasance wurin tarihi ranar 23 ga Afrilu 1959 inda ake kiran wurin da suna Katsina Museum .Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa Firayim Ministan Nijeriya na farko da kuma Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato Firimiyan Arewa duk,sun halarci makarantar.

  • Jami’ar FUDMA Ta Ƙara Fadawa Cikin Rikicin Shuagabanci A Katsina
  • Gidauniyar Mangal Ta Dauki Nauyin Yi Wa Mutum 12,300 Masu Cutar Kaba Aiki A Katsina

An gina Kwalejin ne a kofar sauri wadda take cikin birnin Katsina,kafin dai bayyanar ilimin zamani wanda ake kira da suna Boko,ilimin addiin musulunci a wancan lokacin shi ne ake amfani da shi ne ake amfani da shi.Wannan dalilin shi yasa Turawan mulkin mallaka a wancan lokacin suka fuskanci matsala gare su da suke niyyar shigo da ilimin zamani a lokacin,don  haka sai suka bi lamarin,a hankali inda daga baya suka kafa makarantar Katsina Kwalej a shekarar 1922.

ADVERTISEMENT

Hada Arewacin da Kudancin Nijeriya da aka yi a shekarar shi yasa bukatar ilimin zamani ta taso, bayan shekara ashirin da kasancewar su, ba lokacin bangaren Arewa musamman ma lardunan da suke karkashin ta basu da ‘yan asalin wurin wadanda suke da ilimin zamani sosai da har, za’a iya basu mukamin Akawu su yi aiki a ofisoshin gwamnati da kuma sassan. Gwamnan Arewa  Sir Hugh Clifford,shi ya sa aka kafa Kwalejin domin horar da ‘yan Arewa wadanda za su yi aiki a makarantun Lardunan.

An taba jin Sir Clifford yana cewa lokacin da yake bude makarantar da aka sa ma suna Katsina Kwalej cewa babban dalilin kafa ita makarantar shi ne a koyawa Malamai wadanda, “su ma  a matsayinsu na Malamai a gaba watarana sune za su iya kasancewa Shugabanni,wadanda ana sa ran halayensu na iya gyaruwa domin a daidaita al’umma.”Kwalejin Katsina ta fara ne da daukar dalibai 50  wadanda  suke daga Lardunan Arewacin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi  Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan  Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim,  da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina

An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara. Wannan  shi tun  lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da  hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo  a lokacin.Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shi ya bada wurin da aka gina Katsina Kwalejin ne a cikin gonarsa da ke Rafukka a lokacin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ilimi

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

November 30, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji A Sokoto

Sojoji Sun Kashe Na Hannun Daman Bello Turji A Sokoto

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.