ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Masarautar Zazzau Da Sarakunanta (9)

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
Zazzau

LABARAI MASU NASABA

Tarihin Gambo Sawaba (1)

Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (3)

ADVERTISEMENT

Kamar yadda Mudathir Ishak ya yi tsokaci an kafa birnin Zazzau ne a shekarar 1536, miladiyya,a wani yanki na dausayi, kudu da hamada, maraya ce da ta hada manoma da kuma malamai da masu kasuwanci.Sarkin Farko a wancan lokaci sunansa Gunguma dan Bawo.

Bawo kuwa a Hausance shine Bayajidda na Sarauniyar Daurama. Zariya ita ce kanwa ga Sarauniya Amina shine kuma sunan da ta baiwa babban birnin Zazzau,kusa da dutsen Kufaina,a cikin karni na 16 ne aka sanya wa Zazzau wannan suna.

  • Sojoji Sun Aike Da Ƴan Ta’adda 8 Lahira, Sun Daƙile Yunƙurin Sace Wasu Mutane 28
  • Takaitaccen Nazari A Kan Bishiyar Kanya

Sarauniya Zariya ta gaji Amina wadda rasu a  shekarar 1610 miladiyya a garin Attagara, bayan da ta ci Kano da Katsina da yaki.

Ita ma ta rasu a Yawuri ne, bayan da tayi gajeren mulki. Fadin iyakar inda ta ci da yaki ya kai daga jihar Filato ta yanzu a gabas, zuwa Abuja da kewaye, kamar su Nupe da Nasarawa.

A Arewa kuma har Daura da Katsina ta hadiyo.Ta kuma ta shafe shekaru 30 tana mulki. Mahaifiyarsu ita ce Bakuwa Turunku,ta 22 a jerin sarakunan Zazzau, kafin zuwan fulani. Ita ta kafa garin Turunku, kudu da Zazzau ko Zariya,a kan hanyarta ta zuwa yake-yake da kabilun Nupawa da Gwarawa.Jerin sunayen sarakunan gargajiya da aka yi a Zazzau. Kafin dai fulani su ci Zariya da yaki,a shekarar 1807,an yi sarakuna 60 Hausawa ‘yan asalin garin da yankin, watau sarakunan Habe, wadanda wasunsu sun bi addinan gargajiya, yayin da wasu suka yi addinin musulunci. Sarki Jatau dai a tarihi, wanda yayi mulki ne daga shekarar 1742 zuwa 1802 shi ya fara musulunta ya kuma gina masallaci na farko. Bayan rasuwarsa,sai dansa Makau, ya koma addinin gargajiya, ya kuma rushe masallacin.

Sai dai kuma a shekarar 1804 ce, da Usmanu dan Fodiyo ya fara yin jihadi, Malam Musa,  wanda malami ne kuma bafillace,ya je Gobir inda ya karbo tuta daga Shehu,daganan ya hada karfi da Yamusa, wanda shi ma bafillatanin Borno ne, suka kawo wa Makau yaki. Haka ya sa Makau ya tsere zuwa garin Zuba, inda kusa da inda Babban Birnin Tarayya Abuja take a yanzu, a can ne ya rayu da kabilun yankin har dai ya kai ga rasuwa a can.Malam Musa sai suka tabbatar da abin da mahaifinsa ya faro,watau Masallaci da addinin Islama.

Malam Musa shi ne Sarkin Fulani na Farko, amma ya rasu a a shekarar 1821,daga nan sai Yamusa ya amshi mulki, inda yayi mulki har  ya zuwa shekarar 1834.Daga nan sai Malam Abdulkarim, wanda shi bakatsinene kuma bafillace, ga shi dalibi ga Malam Musa ya karbi mulki.Kuma daga wadannan gidaje ne har yau, ake samar da sarakunan Zariya.1. Mallam Musa (gidan Mallawa) 1804-1821 2. Yamusa (gidan Barnawa) 1821-1834 3. Abdulkarim (gidan Katsinawa) 1834-1846 .4 Hamadu dan Yamusa 1846 5. Muhamman Sani dan Yamusa 1846-1860 6. Sidi Abdulkadir dan Malam Musa 1860 (ture shi aka yi)7.Abdussalami (sullubawa) 1860-1863 8. Abdullahi dan Hamadu dan Yamusa 1863-1873 (an ture shi) sai a 1876-1881 (aka sake ture shi) 9. Abubakar dan Malam Musa 1873-1876 l0. Sambo dan Abdulkarim ( gidan Katsinawa)1881-1890 (shima tumbuke shi aka yi) 11. Yero dan Abdullahi dan Hamadu 1890-1897 12. Kwasau dan Yero 1897-1902 (tumbuke shi aka yi) Zuwan Turawa 13. Aliyu Dan sidi Abdulkadir 1902-1923(shima an tumbuke shi) 14.Dallatu dan Yero 1923-1924 15. IIbrahim dan Kwasau 1924-1936 16. Malam Ja’afar dan Ishak 1936-1959 17. Alamin dan Usman 1959-1975 18.Shehu Idris 1975 zuwa shekarar 2020, daga shi kuma sai Ahmad Nuhu Bamalli wanda aka nada sarauta ranar 8 ga Oktoba 2020 zuwa yanzu.Turawa sun iso da rundunoni na yaki har biyu, a 1900 domin mulkin mallaka.

Jerin sarakunan Suleja da ake kiran su da Sarkin Zazzau Suleja wadanda asalinsu daga can suke.

  1. Muhammadu Makau 1807-1825.
  2. Abubakar Ja (Abuja) 1825-1851.
  3. Abubakar Kwaka Dogon Sarki 1851-1877.
  4. Ibrahim Iyalai Dogon Gwari 1877-1902.
  5. Muhammadu Gani 1902-1917 Ya bar gadon mulki.
  6. Musa Angulu 1917-1944

An samo wannan  Tarihin ne daga encyclopedia ta Hausa

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tarihin Gambo Sawaba (1)
Tarihi

Tarihin Gambo Sawaba (1)

December 7, 2025
Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (2)
Tarihi

Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (3)

November 29, 2025
Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (2)
Tarihi

Tarihin Alhaji Isa Kaita Wazirin Katsina (2)

November 22, 2025
Next Post
Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Kazanta?

Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Kazanta?

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.