Wani babban lamarin da yake vata rai shi ne kananan dakarun Sojan da aka bari su lura da wurin basu samu damar bada wata kariya ba, ga shi Birnin domin kuwa sun yi kadan daga karshe dai an kai ma Timbuktu hari inda aka samu damar mamaye ta.
Turawan da suka tafo daga Turai sun isa Timbuktu a farkon karni na 19.
- Gwamnati Za Ta Inganta Wuraren Tarihi Domin Nishadantarwa A Duk Jihohin NijeriyaÂ
- Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murnar Kammala Aikin Tashar Qinling Dake Antatika
Wani matafiyi daga kasar Scottland Gordon Lain wanda bai samu nasara tafyar ta shi ba,shi ne mutum na farko wanda ya isa a shekarar Gordon Laing (1826), daganan sai wani matafiyi daga kasar Faransa da ake kira da suna Rene- Auguste Caillie a shekarar 1828.Caillié,shi ya koyi yadda addinin musulunci yake da kuma koyon Larabci, bayan da ya isa Timbuktu sai ya nuna shi kamar wani Balarabe ne.Bayan mako biyu ne ya koma wanda shi ne mutum matafiyi na farko wanda ya koma Turai wanda yake da labarin farko na yadda Birnin yake(akwai jita-jita na irin dukiyar da ke Timbuktu wanda kasashen Turai sun san da hakan shekaru masu yawa,hakan kuwa ta faru ne saboda yadda labaran tafiyar Musa zuwa aikin Hajji a karni na 11 da tawagar Rakumma masu yawa da dukiya zuwa Makka).A shekarar 1853 ce wani Bajamushe masanin labarin kasa Henrich Barth ya isa Birnin bayan da yayi tafiya da kafa ta shekara biyar ta nahiyar Afirka.Ya samu nasarar tafiyar ta sa inda daga baya ya rubuta labarin a littafin da ya sa ma suna chronicle na tafiye- tafiyen da ya yi.
Daga karshe dai kasar Faransa ta mamaye Timbuktu a shekarar 1894.Sun gyara Birnin daga lalacewar da ya yi wadda suka same shi Birnin a ciki,amma dai ba hada si hanyar Jirgin kasa ba ko gyara hanya.A shekarar 1960 ce ta kasance karkashi sabuwar kasar Mali wadda ta samu mulkin kanta.
Timbuktu yanzu wata cibiya ce ta mulki wadda take tsakiyar Mali .A shekarar 1990 ce aka dauki matakin yin gyara domin a samu kuvutar manyanb Masallatai uku,wadanda suka fuskanci barazanar Yashi daga kuma lalacewar da suke yi.An samu wata babbar barazana a shekarar 2012 lokacin da ‘yantawayen Tuareg masu samun goyon bayan masu tsaurin ra’ayin addinin musulunci, suka samu damar mamaye Arewacin kasar.Tuareg sun ce wurin nasu ne wanda ya hada da Timbuktu, a matsayin kasar Azaward mai cin gashin kanta. Sai dai kuma abin bai dauki wani lokaci ba inda su masu tsattsauran ra’ayin addini suka fi karfinsu, daga karshe sun kafa irin dokar shari’ar musulunci akan al’ummar da suke zama a wurin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp