Tarihin Tsohon Sifeta Janar Na ‘Yan Sanda Ibrahim Coomassie

Coomassie

Daga Auwal Mu’azu

Ibrahim Coomassie, shi ne babban da a wurin mahaifinsu, fitaccen malami, kuma dan kasuwa wato Malam Ahmadu Coomassie, wanda ya taba zama permanent secretary a ma’aikatar ilimi ta yankin arewa.

Haihuwa da karatu

An haifi Ibrahim Ahmadu Coomassie a jihar Katsina, ranar Larabar, 18 ga watan  March na shekarar 1942.

Ya fara karatu a Central Elementary School Katsina, daga 1950 zuwa 1952. Ya yi Midle School Katsina, daga 1953 zuwa 1954. Ya yi Probincial Secondary School Zaria, daga 1956 zuwa 1961. Ya yi Barewa College Zaria, daga 1962 zuwa 1963. Sannan ya yi wani kwas a Detectibe Training College, Wakefield, da ke kasar Ingila, a 1967. Ya yi  wani kwas Oberseas Officers, a Police Admistration da ke kasar America, a 1973. Ya yi wani kwas na musamman na Security Inbestigation, a Washigtom D.C a kasar America duk a shekarar. A cikin shekarar dai ya yi wani kwas na Militry Intelligence, a Military Institute, duk a America. Ya yi kwas na Instructor’s, a Police Training College da ke kasar Ingila a 1975. Ya yi kwas na Command, a Police Staff College da ke Jos, a 1980. Kana ya yi National Institute for Policy and strategic Study, Kuru Jos, a 1981.

Aiki da gwagwarmayar rayuwa

Ya fara aikin dansanda a shekarar 1991 a matsayin Inspector. A shekarar 1993, Ibrahim Coomassie ya zama Inspector General na rundunar ‘yan sanda ta kasa, a zamanin mulkin General Sani Abacha, bayan karewar wa’adin Aliyu Atta. Shekara daya da kama aikinsa, M.K.O Abiola ya sa aka kama shi ba tare da wata takarda ko bin kowace irin ka’ida ta shari’a ba, haka kuma babu sa hannun hukumar ‘yan sanda ta kasa. Inda aka kai shi gidan yari aka dinga azabtar da shi har tsawon shekaru hudu, bisa zargin aikata laifin kisan kai. A shekarar 1998 ya shaki iskar ‘yanci, biyo bayan mutuwar M.K.O Abiola. Sannan aka mayar da shi matsayinsa.

A shekarar 1996, Commesie ya kaddamar da wani bincike a cikin hukumar ‘yan sanda, bisa irin rawar da suka taka a zamanin mulkin soja, karkashin jagorancin General Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya yi daga shekarar 1985 zuwa 1993.

A watan Yuli na shekarar 1997, Commasie ya ce yana son zai yi wasu tambayoyi ga jakadan kasar America, Walter C. Carrington, tare da dukkan mambobi, da jami’ai na hukumar jakadancin kasar, a game da wasu bayanan sirri da suka fito jim kadan bayan wani harin bomb da aka kai ga rundunar sojoji ta kasa. Jaridar The New Work Times ta rawaito cewa; Gwamnati bata bayyana dalilin da ya sa take son yin tambayoyin ga jakadan na kasar America Walter C. Carrington ba. Amma Inspector General Ibrahim Commassie ya ce; “Babu shakka mun mika bukatarmu ga hukumomin difilomasiyya a kan su bamu damar gabatar da tambayoyi ga jakadan kasar America da sauran membobinsa…”  sai daiAmerica ta ce bata samu wannan sakon ba.

Gwamnatin soja ta zargi babbar kishiyarta wato hukumar National Dimocratic Coalition, kan cewa ita ce ta bayar da umarnin kai harin, wanda ya jawo asarar akalla rayukan mutane goma, tare da jikkata wasu da dama.

A watan March na shekarar 1998, Ibrahim Commasie ya ce jawabin da shugaban gwamnati General Sani Abacha ya gabatar a watan Nuwamba na shekarar 1997, akwai kurakurai a ciki. Ya ce; General Abacha ya yiwa Aminesty International alkawarin sakin wasu firsinoni, amma bai saki wadanda aka daure kawai saboda suna adawa da gwamnatinsa ba. Haka zalika a yayin wani bikin yaye dalibai ‘yansanda, a watan Juli na shekarar 1998, Commasie ya gargadi sabbin ‘yansanda a kan su guji karbar cin hanci da rashawa, sannan ya kara da cewa ya bayar da umarnin a cire dukkan wani shingen kan hanya da ‘yansanda suka sa. Amma duk da haka ‘yansanda sun ci gaba da sanya shingaye a kan hanyoyi.

A cikin shekarar ne dai, Commasie ya yi binciken cewa a kowane lokaci ‘yan kasa zasu iya fara mallakar makamai don ko dai kare kansu, ko kuma fara far ma jami’an tsaro. Matakin farko da ya fara dauka shi ne, samar da wasu kayayyakin tsaro, tare da ba wa jami’an tsaro na ‘yansanda umarnin ba wa gidansa kariya.

A rasuwar shugaban kasa General Sani Abacha, a watan June na shekarar 1998, wadda aka danganta faruwarta ga bugawar zuciya. Ibrahim Commasie shi ne ya jagoranci tawagar kwararrun masu binciken kwakwaf na gwamnatin tarayya, suka ziyarci matar marigayi Sani Abacha, wadda ta zargi daya daga cikin jiga-jigan tawagar da daukar nauyin kisan mai gidan nata, kuma ta umarci Commasie ya kama shi.

A watan January na shekarar 1999, Commasie na daya daga cikin tawagar da gwamnatin tarayya ta tura don su yi shawagi a sararin samaniyar kasar Libya, lokacin da U.N ta dakatar da harkokin sufurin jiragen sama zuwa kasar. Sannan shi ne ke magana da ministan harkokin kasashen wajen kasar ta Libya, Omar Mustafa al-Montasser.

Ibrahim Commasie ya yi ritaya daga aiki tare da barin gwamnati a lokacin mulkin General Abdulsalami Abubakar, a watan May na shekarar 1999.

Karramawa da lambobin yabo

Ya samu karramawa da lambobin yabo masu tarin yawa, wadanda suka hada da; Grand Commander of the order, Silber Jubilee Annibersary Medal, Nigeria Police Medal, National serbice Medal, da dai sauransu da dama. Hakazalika a shekarar 1999, aka nada shi matsayin Sardaunan Katsina.

Kalubale

Kamar kowane mutum a rayuwa Ibrahim Commasie shi ma ya fuskanci  kalubale a rayuwarsa,  domin ko a watan October na shekarar 1999, gwamnati ta gabatar da wani bincike a game da yadda gwamnatin marigayi General Sani Abacha ta gudana, da kuma kisan da aka yiwa uwar gidan marigayi M.K.O. Abiola, wato Kudirat Abiola, wadda aka kashe a ranar 4 ga watan June, 1996. Tare da fadada binciken wanda ake zargin ya kashe Shehu Musa ‘Yar adua, a yayin da yake kulle a gidan yari, a shekarar 1997. Sakamakon binciken da ya sanya aka kame wasu mutane, ciki kuwa har da Ibrahim Commasie, tare da wasu jagororin gudanarwar gwamnatin marigayin, kamar tsohon shugaban rundunar sojoji, wato Lieutanant General Ishaya Bamaiyi, da kuma dan marigayin wato Muhammad Abacha, wanda ake zargin da sa hannunsa a mutuwar Kudirat Abiola.

A lokacin da aka kama Commasie yana cikin gidansa. Wasu rahotanni sun bayyana cewa Commasie ya shigar da kara bisa kamun da aka yi masa, tun ma kafin jami’an bincike na hukumar ‘yansanda ta kasa su gurfanar da shi a gaban kotu, wanda hakan ya sanya mutane ke zargin ko an sake shi.. Amma kimanin watanni guda bayan bayyanar rahotannin, ministan sadarwa na kasa Dapo Sarumi, ya karyata zancen, tare da tabbatar da cewa Ibrahim Commasie yana tsare a hannun ‘yansanda.

Kafar yada labarai ta BBC sun rawaito cewa; “Ministan sadarwa na kasa, Dapo Sarumi, ya musanta rahotannin da ake yadawa cewa an saki mutanen biyu, inda yace Commasie tare da tsohon shugaban rundunar sojoji ta kasa Lieutenan General Ishaya Bamaiyi suna tsare a hannun jami’an tsaro…”

A ranar 14 ga watan August, na shekarar 2004, Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman, ya kaddamar da wasu kwamitoci guda goma sha daya, domin tsayuwa tare da gudanar da aiyukan kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) a jihar ta Katsina, ‘yan kwamitin da suka hadar da; Justice Muhammad Bello, Justice Mamman Nasir, Justice Sadik Mahuta, wazirin Katsina Alhaji Muhammad Lugga, da kuma Ibrahim Commasie da dai sauransu.

Ya zama dan kwamitin amintattu na hadaddiyar kungiyar Arewa Consultatibe Forum reshen jihar Katsina. Kungiyar da ke da manufar kare muradan ‘yan arewa, tare da inganta harkokin kiwon lafiya, da hadin kai da kuma taimakekeniya tsakanin jama’ar yankin.

A watan September na shekarar 2008, Ibrahim Commasie ya gamu da hadarin mota a kauyen Dokawa da ke hanyar Katsina zuwa Daura, inda ya samu muggan raunuka.

Jaridar Leadership ta ranar 18 ga watan September ta rawaito cewa; Tsohon sifeton ‘yansanda na kasa Alhaji Ibrahim Commasie, yana cikin mawuyacin hali, a sakamakon hadarin mota da ya gamu da shi a kan hanyar Katsina zuwa Daura. Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewa an hango kaninsa, tare da wakilan masarautar jihar Katsina a cikin matsananciyar damuwa…

A watan August na shekarar 2009, Commasie ya bayar da gudunmwar miliyoyin kudi, domin a gina dakin karatun dalibai tare da kayan karatu na kimiyya a makarantar Police Boys Secondary School, da ke karamar hukumar Mani, ta jihar Katsina.

Ibrahim Commasie ya rasu a ranar 19 ga watan July na shekarar 2018.  Ya rasu yana da shekaru 76 a duniya. Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya, da kuma ‘yan uwa da dama

Exit mobile version