Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas na gudanar da taro karo na 10 a Bauchi domin tattaunawa kan inganta harkokin tsaro da tattalin arzikin yankin.
Taron dai na da nufin lalubo dabaru da hanyoyin amfana daga albarkatun ƙasa a jihohi shida na Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya bayyana cewa gwamnonin suna aiki tuƙuru wajen bunƙasa tattalin arziki da kuma sauran matsalolin da yankin yake fuskanta kamar na ta’addanci.
Bayan tattaunawa ta farko, sai taron ya rufe ƙofa domin tattaunawar sirri daga bisani kuma za a fitar da sanarwar bayan taro. baya.
Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) na daga cikin masu bayar da gudunmuwa a tattaunawar, bayan kammala taron gwamnonin za su bi sahun mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima domin ƙaddamar da wasu ayyuka a Bauchi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp