Ƙa’idar da masana a fannin ilimin kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar jama’a (Sociologist), musamman waɗanda ɓangaren ƙwarewarsu shi ne laƙantar yanayin ɓarna da aika-aika (Criminology), sun bayyana wani laƙani dangane da kisan kai (murder) da cewa; kashi 90% na dukkanin kisan kai da ke aukuwa a duniya, ya na faruwa ne bayan wanda aka kashe ɗin ya yi cacar baki, samun saɓani ko jayayya da wani. Watanni, makonni ko kwanaki kaɗan kafin a aiwatar da aika-aikar kashe shi.
Don haka ne ma idan a ka yi kisan kai, irin wanda kawai a ke aika wa da Makasa (hire killers) ɗin nan, to masu bincike su kan yi ƙoƙarin bibiyar waɗanda saɓani ya taɓa gifta tsakaninsu da mamacin.
Na buɗe wannan maudu’i ne da kawo misali dangane da kisan kai a ƙoƙarina na son bayyana ɗaya daga cikin manyan munanan ayyukan da fushi ke iya jefa mutum ga aikata su. Wanda kuma a rayuwa na yau da kullum, irin wancan salon aika wa da mutum lahira ya zama ruwan dare.
Fushi ɗabi’a ce mai matuƙar haɗari da tsautsayi, kuma ɗabi’a ce wacce ta samu gurbin zauna wa dindindin a dukkan zukata, sai dai akwai bambanci tsakanin samun gurbin zaman fushi da kuma tasirinshi fushin.
Bilhasali ma, wasu ’yan adam ɗin a maimakon ɗabi’ar fushi ta yi tasiri a zukatansu, sai ya zama cewa su ne suka yi rinjaye akan wannan ɗabi’ar ta hanyar danne ta da sanyin zuciya, sassauci da sauransu.
Wannan gagarumin aiki na danne ɗabi’ar fushi ba kowanne mutum bane zai bushi iska ya iya aikata wa. Sai wanda ya kasance yana da ikon sarrafa zuciyarshi ba zuciyar bace ke da iko a kanshi.
Babban makamin da ke bayar da dama ga ɗan Adam ya iya sarrafa zuciyarshi shi ne ya kasance mai halayen ƙwarai da ɗabi’u masu nagarta. Idan har zai iya tarbiyyantar da zuciyarshi da halaye da ɗabi’u masu kyau, babu tantama zai iya sarrafa ɗabi’ar fushinsa.
Idan za a yi bayanin ɗabi’ar fushi ne a baje a faife dalla dalla, dole ne sai an fara tun daga rayuwar jinjiri har zuwa tsufa. Lokacin da yaro ke jinjiri, a matakin shayarwa, idan yunwa ta ci yaro ko kuma mahaifiyarshi ta fita harkarshi na wani tsawon lokaci, sai ɗabi’ar fushi ta taso ma shi ya fara kuka mai ƙarfin gaske.
A wasu lokutan rashin kulawar iyaye, sai ka ji an fara cewa ‘kai wannan jinjiri akwai rigima’. Alhali kuwa mahaifan ba su san a hankali su na gina zuciyar ɗansu ba ne ta yadda za ta yi ƙarfi wurin tasirantuwa da ɗabi’ar fushi.
Da jariri zai samu kulawa da tarbiyyar mai kyau, zai taso nagartacce sannan kuma kammalalle mai ɗabi’u kyawawa. Wannan ya tabbatar da maganar hausawa da ke cewa, itace tun ya na ɗanye a ke lanƙwasa shi.
Shi fushi suna da alaƙa ta ƙut da ƙut da zuciyar mutum. Duk lokacin da mutum ya yi fushi, zuciyarshi na komawa kashi biyu; kashi na farko, ta na ƙoƙarin kwantar da hankalin mutum, kashi na biyu kuma za ta riƙa ƙoƙarin takura zuciya akan ɗaukar mataki ƙwaƙƙwara.
Ko da tsakanin ɗa da iyayenshi ne, bai kamata mahaifi ko mahaifiya su tozarta ɗansu a gaban mutane ba. idan ɗan ya yi laifi wanda za a tsawatar ma shi. Haƙƙin mahaifan ne su keɓe shi, sannan su bi duk hanyar da su ke ganin itace mafita ga daidaituwar al’amuran yaron.
Amma a lokacin da iyaye su ka sabawa zuciyar ɗansu da tozarci a fili, ɗabi’ar fushin yaron za ta iya tasirantuwa akan zuciyarshi ya faɗi maganganun banza (waɗanda ba su dace ba) ga iyayen, haka nan idan bulala (ladabtarwa) ne iyayen su ke yi wa ɗa a tozarce cikin jama’a, toh su na gurɓata zuciyar yaron ne ta yadda watan wata rana ɗabi’ar fushi za ta sawwala mai haukan ya yi ramuwa.
Da wannan za mu iya fahimta a taƙaice irin gudummawa da rawar da iyaye su ke takawa wurin ginuwar ɗabi’ar fushi ga zukatan ‘ya ‘yansu. Ɗabi’a ce wacce ba a isa a rushe samuwarta ba a zuciya, sai dai a kafa tarkon kashe kaifinta kafin ta yi illa.