Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya dawo Abuja a ranar Litinin bayan halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na 2025 a Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ya karɓi jawabi daga Shugaban Hukumar FIRS, Zach Adedeji, sannan ya gana da Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, da ɗan Majalisar Wakilai, James Faleke.
- Trump Ya Sake Ɗarewa Kan Mulkin Amurka, Sabbin Ƙudirorinsa Sun Bar Baya Da Ƙura
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Samun Ingantar Tattalin Arziki
A yayin taron, Tinubu ya yi bayani kan matakan da Nijeriya ke ɗauka don yaƙi da sauyin yanayi tare da kira ga haɗin gwiwar duniya.
Haka kuma, ya tattauna kan inganta cinikayya tsakanin kasashen Afirka tare da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame, da kuma tabbatar da alaƙa mai ƙarfi da Shugaban Ƙasar Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev.
Tinubu ya yaba wa ƙananan kamfanonin Nijeriya guda biyu da suka yi nasara a gasar Zayed Sustainability Prize saboda ƙirƙirarsu, kuma ya gayyaci Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed, zuwa Nijeriya, wanda ya amince da gayyatar.