Shugaba Bola Tinubu ya gana da Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), a fadar shugaban kasa da ke Abuja da yammacin ranar Laraba.
Ko da yake har yanzu ba a san takamaiman abin da aka tattauna a taron ba, mai yiwuwa abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun yi tasiri a taron.
Kimanin sa’o’i 24 da suka gabata a ranar Talata, jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) suka tare ginin ofishin EFCC na Legas.
LEADERSHIP ta tattaro cewa lamarin da ya faru a ofishin EFCC da ke Legas na daga cikin batutuwan da shugaba Tinubu da shugaban EFCC suka tattauna yayin ganawar.
Idan dai za a iya tunawa, nan take shugaba Tinubu ya umarci hukumar DSS da ta janye jami’anta da ababen hawansu daga ofishin EFCC domin mayar da martani ga arangamar.
Ya kuma kara jaddada bukatar warware duk wata rashin fahimta da ke tsakanin hukumomin biyu.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Tunde Rahman ya fitar, shugaba Tinubu ya umarci ma’aikatan gwamnatin tarayya da su bar ofishin EFCC da ke Ikoyi a Legas, bayan samun rahoton da hukumar DSS ta yi wa ginin.
Matsayin shugaban ya ta’allaka ne kan warware duk wata matsala da ke tsakanin manyan hukumomin gwamnati ta hanyar da ta dace.