Bayan nasarar da ya samu a wajen taron ‘Sabuwar Yarjejeniyar Kudade ta Duniya’ da aka yi a birnin Paris na kasar Faransa, wanda Shugaba Emmanuel Macron ya karbi bakunci, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Bissau, babban birnin Jamhuriyar Guinea-Bissau, domin halartar taro na 63 na shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).
Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da damar taron wajen ziyartar rundunar sojojin Nijeriya da ke kasar a karkashin kungiyar ECOWAS.
- Gwamnatin Gombe Ta Sha Alwashin Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya
- Sharhi: Sin Da Amurka Ba Su Bukatar Zama Abokan Gabar JunaÂ
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake ya fitar, ya ce taron na 63 da zai gudana a ranar Lahadi 9 ga watan Yulin 2023, zai kasance karo na farko da shugaban kasar zai gudanar da harkokin kasa da kasa a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Shugaba Tinubu, wanda jirginsa ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Bissau da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar, ya kasance abun jan hankali.
Ana sa ran shugabannin yankin 16 za su yi jawabi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi yankin da suka hada da rahoton zaman taro na 50 na kwamitin sulhu na MDD wanda ya kunshi kalubalen tsaro da kasashe mambobin kungiyar ke fuskanta.
Sauran batutuwan da shugabannin za su tattauna sun hada da rahoton halin da ake ciki a Jamhuriyar Mali, Burkina Faso da Guinea.
Bayan isowarsa, shugaba Tinubu ya ziyarci dakarun Nijeriya karkashin kungiyar ECOWAS da ke kasar Guinea-Bissau.
Ya bayyana godiyarsa ga sojojin da kwamandansu Janar Al-hassan Grema bisa sadaukarwa da hidimar da suke yi wa Nijeriya da kuma kasar da ta karbi bakuncinsu, ya kuma kara da cewa Nijeriya za ta ci gaba da tallafawa dimokuradiyya a yammacin Afirka da ma duniya baki daya.
“Na zo nan ne domin nuna goyon baya a gare ku, ina so in tabbatar muku cewa mun kuduri aniyar tallafawa zaman lafiya da dimokuradiyya ba kawai a yammacin Afirka ba har ma a duniya baki daya.
“Nijeriya kasa ce da ta yi kaurin suna a Saliyo da Laberiya da sauran wurare, muna fatan za ku goyi bayan kare tsarin mulkin kasa.
“Muna alfahari da ku, muna alfahari da amincinku, Nijeriya ta dogara da ku, za a samu zaman lafiya da ci gaba a kasarmu,” in ji shugaban.
Birgediya Janar Grema ya bayyana jin dadin sojojin ga shugaba Tinubu saboda kasancewarsa babban kwamanda na farko a tarihin Nijeriya da ya ziyarci sojojinsa a wajen gabar tekun kasar.
A yayin da yake ziyara a kasar Guinea-Bissau, shugaban na Nijeriya zai gudanar da tarukan kasashen biyu tare da yin wasu ayyuka a gefen taron.
A cikin tawagar shugaban kasar a wannan tafiya akwai mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, mukaddashin gwamnan babban bankin kasa, Dokta Folashodun Shonubi; Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa; Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro, Dokta Ibrahim Kana; Babban Sakatare na Ma’aikatar Kudi, Aliyu Ahmed da Wakilin ECOWAS, Ambasada Musa Nuhu.
Sauran da ke cikin tawagar sun hada da tsoffin gwamnoni, Sanata Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi), Abdullahi Ganduje (Kano), Abubakar Badaru (Jigawa) da kuma Sanata Abu Ibrahim daga jihar Katsina.