Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai zaɓi wanda zai yi masa mataimaki a zaɓen 2027 ba sai bayan babban taron jam’iyyar APC da za a gudanar a 2026.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan dabarun watsa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Daily Trust, inda ya ce tsarin dimokuraɗiyya na ainihi yana buƙatar a fara da ɗan takara kafin a sanar da mataimaki.
- Ganduje Ya Noƙe Kan Furta Ko Shettima Zai Yi Takara Da Tinubu A 2027
- Dalilin Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare da Ambaton Shettima Ba – Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas
Onanuga ya ƙaryata jita-jitar cewa akwai wani shiri na cire Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima daga tikitin 2027, yana mai cewa babu wata matsala tsakanin Tinubu da Shettima, kuma suna da kyakkyawar alaƙa ta aiki. Ya ce batun musulmi da musulmi a matsayin tikiti bai kamata ya sake zama matsala ba, ganin cewa tun da farko ba a sami wata barazana ga rayuwar Kiristoci a Nijeriya ba.
A baya dai an sami zazzafar muhawara a taron APC na yankin Arewa maso Gabas a Gombe, inda rashin haɗa sunan Shettima cikin jerin goyon bayan da ake baiwa Tinubu ya haifar da cikas. Duk da haka, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya sake bayyana cikakken goyon bayansa ga Shettima, yana mai cewa rawar da ya taka a gwamnatin Tinubu na da matuƙar tasiri ga cigaban ƙasa.
Shugaban APC na Arewa maso Gabas, Salihu Mustapha, wanda ya ƙi mara wa Shettima baya, ya ce yana bin ƙa’idar jam’iyya ne da tsarin zaɓe. Ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa ne ke ƙoƙarin kawo husuma tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ake gani a kusan kowanne mataki na siyasa a Nijeriya.
A nasu ɓangaren, ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi, MURIC, ta gargaɗi APC da Shugaba Tinubu da kada su sauya Shettima a matsayin mataimaki a 2027.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce duk wani yunkuri na cire Shettima zai zama matakin da bai dace ba kuma ya kamata a nemi shawara daga manyan masu ruwa da tsaki kafin ɗaukar kowanne mataki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp