Rabiu Ali Indabawa" />

Trump Da Kim Za Su Gana A Singapore

Kafofin yada labaren Koriya ta kudu sun bayyana cewa maiyiwuwa taron koli tsakanin shugaba Donald Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai kasance a wata mai zuwa a kasar Singapore.

Jaridar Chosun Ibo da kafar yada labaran Yonhap sun fada tare da kin bayyana majiyoyin su, cewa Amurka da Koriya ta Arewa sun yarda cewa taron zai kasance a cikin sati na uku a na watan Yuni domin gujewa cin karo da taron manyan kasashe duniya bakwai wato G-7 wanda za a yi a kasar CANADA a ranakun 8 da 9 na watan Yuni wanda kuma shugaban na Amurka zai halarta.

Trump ya shaida wa manema labarai a ranar jumma’a cewa bangarorin biyu na da rana da kuma wurin haduwar tasu. A baya ne dai ya ce yankin da babu soji dake tsakanin kasashen Koriya biyu zai iya zama wuri mai kyau domin ganawar tasu.

 

 

An rantsar da Bladimir Putin a wani sabon wa’adi na hudu na shugabancin Rasha bayan nasarar da ya yi a zaben watan Maris.

Baki dubu biyar ne suka halarci bikin rantsar da shi da aka yi a kasaitaccen dakin taro na Kremlin inda ak rantsar da shi.

Shugaban zai tsawaita shekara 18 da ya shafe yana mulkin kasar, wanda magoya bayansa ke cewa ya farfado da martabar kasar a duniya, yayin da ‘yan hamayya ke bayyana mulkinsa da ta kama karya.

A ranar Asabar da ta gabata, aka samu yamutsi tsakanin masu zanga-zangar adawa da salon mulkin shugaban da jami’an tsaro Sama da Mutum dubu daya aka cafke a biranen kasar 19 lokacin zanga-zangar.

Putin zai karbi rantsuwar kama aiki ne a dandalin da aka nada tsofaffin sarakunan Rasha, a kasar da ta fi kowacce fadin kasa a duniya, kuma za a takaita shagulgula.

Rahotanni sun ce wadanda suka ba da gudunmawa a lokacin yakin neman zaben Mista Putin, mai shekaru 65, ne kawai za su halarci bikin rantsar da shi.

Shugaba Bladmir Putin na fuskantar adawa daga ciki da wajen kasar

Mista Putin na fuskantar manyan kalubale da kuma takukuman karayar tattalin arziki da tasirinsu ke bayyane.

Rasha na ci gaba da fuskantar rikicin diflomasiya da kasashen yamma a kan kasar Ukraine da Syria da kuma zargin da ake ma ta na kutse a harkokin zaben kasashen ketare.

 

Exit mobile version