MUHAMMAD ADAM YARIMA, ya shafe akalla sama da shekara 20 yana sana’ar Burodi. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ABUBAKAR ABBA, ya yi tsokaci a kan kalubalen da gidajen burodi a Jihar Kaduna ke fuskanta, sakamakon tashin gwauron zabi da farashin fulawa ya yi tare da shirye-shiryen da wasu gidajen Burodin ke yi na rufe gidajen da kuma barazanar da ke kunno kai na samun rashin aikin yi da sauran makamantansu. Ga dai yadda tattaunar tasu ta kasance:
Farashin fulawa na ci gaba da hauhawa, wane hali gidajen Burodi suka samu kansu yanzu?
Da farko dai, duk wanda ya kwana ya tashi a Nijeriya, ya san halin da kasar take ciki, domin tun a lokacin da aka ce farashin man fetur ya karu; kusan farashin komai sai da ya karu. Yanzu fulawa ta zama gwal, ba kuma a yin Burodi sai da ita duk da cewa a kwanan baya, an yi kokarin samar da hanyar da za a rika sarrafa Burodin ba tare da dogara da ita ba, amma sai abin ya faskara.
 Gaskiyar Magana ita ce, masu gidan Burodi, musamman a nan Jihar Kaduna, suna cikin mawuyacin hali. Fulawar da a baya ake sayen buhunta daya a kan naira 23,000 zuwa 24,000, yanzu ta naira 29,000; wannan mai saukin kudi kenan, amma mai kyau tana kai wa har naira 32,000.
Duba da wadannan matsaloli da ka jero, yanzu wane hali wannan masana’anta take ciki?
Ko shakka babu, maganar da ake a halin yanzu gidajen Burodi da dama a jihar na rufe, ba sa iya yin aiki. Sannan, akwai gidajen Burodin da suke a nan cikin kwaryar Kaduna, akalla sun kai kimanin 50 da aka sa su a kasuwa za a sayar. Idan ka ga mutum na aikin Burodi yanzu, babu shakka mai karfin gaske ne, kusan masu karfin a da su ne suka koma kanana yanzu, wani lokacin a yi aiki a samu riba, wani lokacin kuma a samu faduwa, amma
saboda sana’ar da aka iya kenan, shi ya sa ake jurewa ake ci gaba da yi.
Har ila yau, ina tabbatar maka da cewa, ko a yanzu akwai masu gidajen Burodin da suke shirin rufewa. Ba wai maganar fulawa ake yi kadai ba, har da batun duk wani abu da ka sani ana hada Burodin da shi farashinsa ya karu, duk wadannan abubuwa ne wadanda kai tsaye suke shafar masu sana’ar gidajen Burodin.
Idan aka ci gaba da rufe wadannan gidajen Burodi kamar ya ka bayyana, mene ne makomar ma’aikatan da suke yi muku aiki?
Wannan ai a bayyane yake, in dai har za a ci gaba da rufe wadannan masana’antu, ya zama wajibi a samu karancin ayyukan yi, domin idan har kana neman wata hanya da mutane za su taimaki kansu da iyalansu musamman ma matasa, sai ka sama musu abin yi. Wannan sana’a ta Burodi tana matukar taimakawa, musamman a bangaren matasa wajen samun kudaden da za su rika tallafa wa kawunansu, ba tare da dogaro ga wani ko iyayensu ba, wani lokacin ma har ‘yan’uwansu suna taimakawa.
Haka nan kuma, yanayin da ake ciki yanzu ya sa masu gidajen Burodin ba su da wani zabi, illa kara farashin kudin Burodin; domin a halin da ake ciki, sai dai kawai a ce innalillahi wa’inna ilaihir raji’un. Domin kuwa yanzu, idan za ka yi tuwo a gidanka, sai ka kashe kusan akalla naira 2,000, amma idan kana da Burodinka da dan kayan shayi, komai sai ya ishe ku. Yanzu idan mun kara wa Burodin farashi, wane irin yanayi kenan mutane za su shiga.
Shi kansa mai sana’ar Burodin da ya zamar masa dole ya kara farashin Burodin sai abin ya shafe shi, domin idan har mutane suna kara bukatar Burodin, gidajen Burodin kasuwarsu za ta kara yin sama. Amma idan ta kai mutane ba sa iya saye saboda karin farashi kasuwar za ta yi kasa, idan kuma kasuwar ta yi kasa sarrafa Burodin shi ma zai yi kasa, kuma ba lallai ba ne a samu kudin da har za a iya juyawa a yi wani aikin daban ba.
Ina mafita dangane da wadanan dinbin matsalolin da ka ambata?
Mafitar ita ce, gaskiya dai kusan sai gwamnati ta kawo mana daukin gaggawa a wannan fani, domin idan akwai wata sana’ar da ake yi yanzu a kasar nan, wadda ba a tsayawa ana jiran gwamnati, kusan zan iya cewa ita ce wannan sana’a ta Burodi; domin kuwa tana daya daga cikin sana’oin da zai yi wuya ka ji an ce wani mai gidan Burodi ya je ya roki gwamnati ta taimaka masa da wani abu, sai dai ma su masu gidan Burodin ne suke taimaka wa gwamnatin, wajen sama mata da kudaden shiga da daukar marasa aikin yi, musamman matasa da sauransu.
Babbar masalahar da za a iya cimma kan wadannan matsaloli su ne, ya zama wajibi gwamnatoci, musamman gwamnatin tarayya ta yi hobasa wajen kawo wa gidajen Burodi daukin gaggawa, domin a gaskiya muna bukatar tallafi, idan kuma har aka bar mu a cikin wannan yanayi, tabbas su ma sauran al’umma za su fada cikin irin yanayin da muke ciki.
Sannan, kar a manta al’umma sun zabi wannan gwamnatin ne, bisa yakinsu na za su samu saukin rayuwa na yanayin da suke a ciki. Tabbas ya zama wajibi, gwamnati ta tallafa wa masu gidajen Burodi, domin mu ba masu dogon buri ba ne, duk yadda aka tallafa mana in sha Allah za a ga sauyi. A yanzu masu gidajen Burodi bukatarsu; ba wai lallai samun wata kazamar riba ba ce illa kawai; mu samu kudi mu kara juya su a cikin sana’ar.
Har wa yau, idan kana neman wanda ake bi bashi a halin yanzu, in ka samu mai gidan Burodi magana ta kare, saboda masu sayar mana da fulawa suna yin kokari matuka, domin za su iya ba ka bashin buhun fulawar da za ka iya samu ka yi aiki, idan bashin masu ba mu fulawar ya yi yawa a kanmu, a karshe muka gaza biya, sai dai a sayar da gidan Burodin a biya bashin. Saboda haka, ka ga akwai matsala, shi yasa akwai matukar bukatar gwamnati ta kawo mana dauki ta hanyar tallafa mana, domin mu samu mu fita daga cikin wannan yanayi da muke ciki.