ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsakanin Ɗanwake Da Danbu Da Ɗangauda, Wanne Ya Fi Maka Daɗi?

by Muhammad Bakir Bello
2 weeks ago
Ɗanwake

Muhawararmu da wannan makon, a kan Ɗanwake da Dambu da kuma Ɗangauda ne, muka nemi jin ra’ayoyinku, domi sanin wanda ya fi muku daɗin ci a rayuwar yau da kullum. A wannan karon ma, SANI ANWAR da MUHAMMAD BAƘIR ne, suka tattaro ra’ayoyin naku.

Zaharaddeen Lawan, daga Kano

Gaskiya tun ina yaro, Ɗanwake da Ɗangauda ba su dame ni ba, ba kuma ni kaɗai ba, har da mahaifiyarmu da sauran ƴan’uwana. Amma Dambu kuwa, abu ne da muke cin sa a marmarce, muke kuma jin daɗinsa ƙwarai da gaske.

ADVERTISEMENT

A duk lokacin da aka yi Ɗanwake a gidanmu, kaɗan muke iya ci, shi yasa dole sai mun sake samun wani abincin da za mu ci. Amma idan Dambu ne, wannan lafiya lau, haka za mu ci mu a marmarce, tanɗe kwano.

Rabi’u Nasiru, daga Kano

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A rayuwata, ina matuƙar son Ɗauwake. Ɗanwake, abinci ne da ba na gajiya da shi kwata-kwata, musamman saboda harkar mai da yaji. Amma Dambu, saurin ginsa ta yake yi, ban a iya cin sa da yawa a matsayin abinci, Ɗanwake kuwa, bayan na ci sai na nemi ƙari.

Ɗangauda shi ma, ina son sa sosai, amma ba kamar Ɗanwake ba. Domin shi ma kusan zubin Ɗanwaken yake da shi, ana cin sa da mai da yaji, amma Ɗanwake na daban ne magana ta gaskiya, shi yasa na fi son sa, na kuma fi cin sa.

Yusif Salisu, Ɓaure Jihar Katsina

A haƙiƙanin gaskiya, na fi son Ɗangauda, abincin da wasu kan kira shi da ‘Ƙato da lage’. Kamar yadda ake haɗa kayan Ɗanwake, shi ma haka ake haɗa shi, ɗan bambancin kaɗan ne.

Ana haɗa kayan haɗin Ɗangauda ne da dawa, wake ko rogo ko kuma a haɗa su baki-ɗaya. Bayan an kammala kwaɓawa da ruwa, sai a samo ganyen Kalgo wanda aka fi sani da ganyen Ɗangauda, a riƙa sa shi a ciki, kafin a kai ga dafawa. Sannan, an fi cin sa da miyar taushe.

Mahadi Isa Waziri, daga Zaria

Na fi son Ɗangauda, musamman idan aka yi masa miyar taushe mai daƙi. Kamar yadda aka sani ne, shi ba kamar Dambu ko Ɗanwake yake ba, ko kaɗan ba ya saurin ginsar mutum.

Haka zalika, ina matuƙar son Dambu shi ma sosai fiye da Ɗanwake. Koda-yake, Danwaken ma ina cin sa, yana kuma yi min daƙi.

Asma’u Aminu Shamsuddin, Abuja

Wallahi Ɗanwake ya fi min daɗi, ba tare da wata gardama ba,

Duba da cewa; Ɗanwake yana da wani asiri na daban. Da farko dai, yana da laushi kamar audiga a baki, sannan kuma sai an zuba masa mai da yaji, albasa, tumatir da kuma kabeji a kai.

Amma Dambu, shi a bushe yake kawai kamar kana cin yashi. Ɗangauda kuwa, yana da wuya yara ƙanana su iya cin sa,

Ɗanwake kuwa, ko tsoho ko yaro ko kowa da kowa na iya ci, shi ne abincin da ke kawo jama’a tare, misali a gidan aure, suna ko biki, musamman waɗanda ba su da wadata.

Khadija Bello Hamza, Zaria

Ɗanwake shi ne abincin gida, wanda babu kamar sa. Gaskiya ina matuƙar son abincin da zai sa yara su zauna tare suna ci. Danwake ne kawai yake da daɗin ci tare. Ina yi wa yara na bakwai da safe, sai na zuba mai, yaji albasa, kabeji da dafaffen ƙwai a ci, sai dai ka ji kowa yana cewa; “Mama a ƙara min”.

Danbu kuwa, yara ba su damu da shi ba ko ma na ce kwata-kwata ba sa son sa. Sau da yawa, sai ka ji yara suna cewa, yana kama da magani. Ɗangauda kuma, yana da wuya ƙaramin yaro ya iya tauna shi, saboda taurinsa.

Amma Ɗanwake, ko mai ciki ko mara lafiya duk suna iya ci. Yana da sauƙi a ciki, kuma yana ba da kuzari, shi ne abincin da ke nuna mace ta san girki.

Adam Bello, Kaduna

Batu na gaskiya, dukkaninsu suna da lokacinsu, amma idan za ka tambaye ni wanne ya fi daɗi, sai na ce Danbu da jar miya ko da ƙuliƙuli.

Shi Dambu, yana da abubuwan da suke ƙara lafiya, kamar gyaɗa, ganye da sauransu. Amma Ɗanwake, idan mai ya yi yawa, yana da illa a jikin mutum.

Ɗangauda, sabon abinci ne wanda Fulani suka kawo mana, Dambu kuma, na talakawa ne. Amma Danwake, tun Shehu Usman Ɗan Fodio muna cin sa. Yana da tarihi, yana da kuma daraja.  Don haka, duk da cewa; ina cin Ɗangauda lokaci zuwa lokaci, amma zuciyata ta fi karkata a kan Dambu.

Hajara Hamisu, Zariya Jihar Kaduna

Ni yarinya ce mai aiki. Don haka, ba ni da lokacin zama ina cin abinci a kwano.

Ɗangauda shi ne abincin, “on the go”. Ina iya nannaɗe shi, in shiga mota da shi, na ci yayin da nake tafiya aiki. Yana da laushi da kuma daɗi. Ba ya wargajewa kamar Ɗanwake.

Dambu yana buƙatar faranti da cokali da ruwa. Danwake kuma idan ya wuce awa biyu, sai ya fara wari. Amma Ɗangauda, awa 24 yana nan lafiya lau, babu abin da zai same shi. Sannan kuma, yana da firotin a jikinsa. Yana kuma gamsar da ni tare da ba ni kuzari, har zuwa in tashi daga aiki. Don haka, shi ne ya fi dacewa da rayuwar birni.

Ɗanwake
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Zamo Babbar Kasa Mai Gudanar Da Hada-hadar Saye Da Sayar Da Kayayyaki

Sin Ta Zamo Babbar Kasa Mai Gudanar Da Hada-hadar Saye Da Sayar Da Kayayyaki

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.