A shekarar bana, yawan cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da karuwa a daukacin fannonin shige da fice, kuma saurin karuwar yawan kayayyakin da aka shigo da su cikin kasar Sin, ya fi na karuwar yawan wadanda aka fitar daga kasar zuwa sassan kasa da kasa a watanni 5 a jere. Wannan sakamako ya shaida yadda kasar Sin ta zamo babbar kasa mai gudanar da hada-hadar saye da sayar da kayayyaki a duniya.
A watanni 7 na farkon shekarar bana, yawan kayayyakin da aka shigar cikin kasar Sin ya karu da kaso 22 cikin dari, kan na makamancin lokaci na bara. A rabin farko na bana kuwa, yawan kudin kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin ya kai yuan tiriliyan 10.74, adadin da ya zarce yuan tiriliyan 10 a karon farko a wannan fage a tarihi. Kazalika, kasar Sin ta riga ta dauki matakin soke harajin kwastam ga kasashe 63, ta kuma zamo muhimmiyar kasa da kasashe da yankuna kimanin 80, suka fi zabar fitar da kayansu zuwa cikinta. Sin ta zama kasuwa mafi girma ta biyu a duniya, a fannin shigar da kayayyaki cikin shekaru 17 a jere.
Daga jiya Juma’a, sauran kwanaki 75 a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigarwa kasar Sin karo na 9. Kuma rahotanni daga hukumar shirya bikin, kamfanoni fiye da 1,300 daga kasashe da yankuna 104 na duniya za su halarci bikin, inda fadin wurin gudanar da bikin zai zarce muraba’in mita dubu 350, kana bikin zai shafi fannonin fasahar AI, da na kiyaye muhalli, da harkokin dake shafar tsoffi da yara da sauransu, kana za a bude sashen kayan Asiya da Afirka na musamman, ta yadda za a kai ga fadada shigar da kayayyaki daga kasashe masu tasowa na duniya zuwa kasar Sin.
Hukumomin kasa da kasa da dama sun bayyana cewa, kasar Sin tana kiyaye fadada kasuwancinta, don samar da gudummawa ga tabbatar da samar da kayayyaki, da fadada cinikayyar duniya baki daya. (Zainab Zhang)














