A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Nijeriya sun shiga rudani bisa tsegunta yiwuwar kai harin ta’addanci daga ofishin jakadancin Amurka tare da gargadi ga Amurkawa da kuma al’ummar Nijeriya.
Gargadin farko ya fito ne ranar 23 ga watan Oktoba wanda suka yi wa taken “Matsalar tsaro – Karuwar Barazanar Kai Harin Ta’addanci,” inda sanarwar ta bayyana cewa, akwai tsananin yiwuwar za a kai harin ta’addanci a Nijeriya musamman ma a Abuja Babban Birnin Nijeriya.
- Hadin Gwiwar Sin Da Pakistan Mai Karfi Ta Haifar Da Sabbin Sakamako
- Sin Ta Sanar Da Shirin Bunkasa Fasahar VR
Ta kuma kara da cewa, wuraren da za a iya kai wa harin sun kunshi, gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan shaguna na zamani, otal-otal, gidajen shan barasa, gidajen abinci, filayen wasanni, ofisoshin jami’an tsaro da kuma cibiyoyin kasashen waje.
Kwanaki biyu bayan wannan sanarwar, sai ga shi Ofishin ‘US State Department’ ya umarci ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka wadanda ayyyukansu ba su da matukar muhimmanci su gagauta ficewa daga Nijeriya tare da iyalansu, saboda tsananin yiwuwar kai hare-haren ta’addancin a Abuja. Daga nan ne kasashen Birtaniya, Jamus, Austreliya da Kanada suka bi sahu inda suka umarci ‘yan kasashen nasu su kaurace wa tafiye-tafiye zuwa Abuja.
Hakki ne na kowacce kasa ta tabbatar da kare mutunci da lafiyar ‘yan kasashenta a duk inda suke a fadin duniyar nan. Muna sane da cewa, Amurka ta bayar da kwatankwacin irin wannan gargadin ga ‘yan kasarta da ke kasashen Ekuatorial Guinea, Chadi da Afrika Ta Kudu kusan a lokaci daya, Allah kadai ya san dalilin yin haka.
Abin da muka kasa fahimta a nan shi ne, shin jami’an gwamnatin Amurka sun mika wa rundunonin tsaron Nijeriya cikakken bayanan sirrin na tsaro da suke a hannun su, duk kuwa muna sane da cewa, ita gwamnatin Amurka ta fi muhimmantar da rayuwar al’ummarta fiye da ta kowanne mutum a duniya.
Amma kuma a wannan duniyar da matsalar tsaro ke kara ta’azzara muna ganin tattaunawa tare da mika bayanan tsaro ga sauran jami’an tsaro abu ne mai matukar muhimmanci, saboda samar da tsaro a fadin duniya hakki ne na dukkan al’ummar duniya gaba daya.
Yanayin lafuzzan da ke tattare da sanarwar gargadin ya sanya ana tunanin ko dai Amurka ta fitar da sanarwa ne a cikin gaggawa wanda hakan kuma ya sanya za a iya tababa a kan sahihancin wannan bayanai na sirri da tunanin cewa Amurkan na gaggawar bukatar ganin wani bala’i ya fadawa Nijeriya kamar dai yadda ta yi hasashen rugujewar Nijeriya kafin ko bayan zaben shekarar 2015, amma gashi ta sha kunya.
A wannan karon, kwanaki bayan gargadin da kuma faifan bidiyon da ke nuna ‘yan Amurka na rububin ficewa daga Nijeriya ta filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe Abuja. Al’ummar Babban Birnin Tarayya Abuja na zaune cikin firgici, rahotanni da ke cewa an kama wasu gungun ‘yan ta’adda a yankin bai taimaka ba wajen kwantar da hankalin al’umma gaba daya ba.
Wasu manyan-manayn harkokin kasuwanci sun rufe yayin da iyalan mazauna Abuja da suke a wajen Abuja suke ta biyiyar su don sanin halin da ake ciki ta sakonnin ta kafafen sadarwa na zamani. Duk da ana samun karin kwanciyar hankali ana kuma tattare da jiran ko-ta-kwana na aukuwar bala’in da aka yi hasashen zai faru. Mutane da dama na daukar duk hasashen da Amurka ta yi to babu tantama sai ya faru.
Watakila a daidai wannan lokacin ya kamata mu tunatar da kanmu cewa, da yawa daga cikin masifun da da duniya ke fuskanta a yau, musamman a cikin shekaru 30 da suka wuce ya faru ne saboda sakaci na gwamnatin Amurka, muna iya tunawa da lokacin da Amurka da kawayenta suka ce wai akwai makaman kare dangi a Iraki.
Duniya ta fuskanci asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da dama, sai daga baya aka sanar da mutane cewa an yi yakin ne tattare da bayanann sirri na karya: babu makaman kare dangin da ake Magana, karya ce kawai aka yayata a duniya a kan lamarin. Abubuwan da suka faru a Libya, da kuma yadda Amurka ta yi gaggawar fita daga kasar Afghanistan ya kamata su sanya Amurka dama duniya kara natsuwa tare da tababan wannan rahoton.
A yayin da wasu kungiyoyin ‘yan mazan jiya ke nuna damuwa a kan abubuwan da suka shafi ‘yan gudun hijira da kuma yadda ake amfani da kafafen sadarwa na zaman zai iya taimakawa wajen sanya rudani a cikin kasar da ta fi kowacce kasa a Afrika wanda hakan ba zai taba zama alhairi ga zata ba da ma duniya baki daya musamman ma abokan gwamnatin na Amurka.
A bayyane yake cewa, gwamnatin Muhammadu Buhari ba zai iya mika aikin tabbatar da tsaron kasa ga Amurka ko wata kasa ta daban ba. Dole Shugaba Buhari ya ji kunyar yadda jami’am tsaronsa suka dauki lamarin gargadin da Amurkan ta bayar, hakan kuma ya sanya duk da neman da shugaban ya yi na al’umma su kwantar da hankalinsu amma al’umma suna nan a cikin fargaba.
An zabi Buhari ne shekara 7 da suka wuce saboda kasancewarsa tsohon soja, al’umma da dama sun yi imanin cewa, zai cika alkawuransa na ceto kasar nan daga kangin ayyukan ‘yan ta’adda da ta’addanci gaba daya.
Ana iya cewa, yadda gwamnatinsa ta fuskanci lamarin harkokin ‘yan ta’addan ya kunyata masu tsananin goyon bayansa, sun kunyata a kan yadda Buhari ya kasa biyawa dimbin masu goya masa baya bukatarsu. Yadda ya tafiyar da al’amarin fasa gidan yarin Kuje da ‘yan ta’adda suka yi inda wasu ‘yan kungiyar Boko Haram da dama suka tsere ya sanya al’umma masu yawa cikin zullumi.
A karkashin mulkinsa ne al’amarin masu garkmuwa da mutane ya zama ruwan dare a Nijeriya, haka kumma siyasar addini da kabilanci ta mamaye harkokin rayuwar Nijeriya.
Duk da haka kuma sai gashi tabbatar da zaman lafiya a yankin Afrika ta Yamma ya kara tabarbarewa saboda karuwar shugabannin sojoji da aka samu ta hanyar juyin mulki, duk da cewa Nijeriya ce, kasar da ke shugabantar sauran kasashe a yankin, matsalarta ta cikin gida ta sanya ta kasa bayar da shugabanci nagari kamar yadda ake bukata.
A dalilin wadannan matsalolin tsaron da Nijeriya da kuma yankin Afrikia ta yamma ake fuskanta ya sa muke ganin bai kamata ofishin jakadancin Amurka ya fitar da wannan gargadin a halin yanzu ba.
Wannan gargadin ba komai zai haifar ba sai dai ya kai ga masu zuba jari daga kasashen waje su kauracewa Nijeriya haka kuma na iya bude fagen yadda za a kara zafafa satar Albarkatun Man Nijeriya.
Amma ya kamata Amurka ta fahinci cewa, duk da tana daga cikin kasashe da suka fi sanin yadda za a fuskanci al’amurar ‘yan ta’adda, ya kamata su fahinci cewa al’amarin ta’addanci ya zamma ruwan dare da kasashe da dama na duniya.
Adaida lokacin da gargadin matsalar tsaron ke cigaba da yaduwa a Nijeriya sai gashi Mr. Paul Pelosi, mijin shugabar Majalisar Wakilan kasa Amurka, Nancy ya fuskanci mummunar hari a gidansa da ke San Francisco kamar dai abin da ya faru na ta’addanci a ranar 6 ga Janairu na shekarar 2021 da aka kai hari fadar shugaban kasar Amurka Capitol.
A wannan shekarar kawai, jaridar New York Times ta ruwaito cewa, an samu hare-haren ‘yan bindiga akalla har sau 531 a Amurka, daga watan Janairu zuwa tsakiyar watan Oktoba.
A ra’ayinmu, ai lamarin ba zai taimaka ba in har ofishin jakadancin Nijeriya da ke Amurka zai bayar da gargadin matsalar tsaro a kan yadda aka samu hare-harbe har sau 53 a duk wata a wata cikin wata daya kawai. Ko kuma ofishin jakadancin Nijeriya da ke a Birtaniya za fitar da gargadin yiwuwar ta’addanci yayin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar inda jaridar Telegraph ta sanar da cewa, an samu fiye da hari 45,391 a Ingila da yankin Wales ya zuwa karshen watan Maris na wannan shekarar.
Duniya ta kara zama wuri mafi hadari a halin yanzu, mutane na amfani da ci gabar kimiyya da fasaha da ake da shi wajen aikata mau’o’in ta’addanci a sassan duniya bag tare da la’akari da wani banbanci ba.
Dole mu yi amfani da dukkan abubuwan da ke a gaban mu wajen tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya.
Dole Amurka da abokananta su mika wa jami’an tsaron Nijeriya dukkan bayanan sirrin da ke a hannun su, su kuma rungumi aiki da jami’an tsaron namu don samar da zaman lafiya a wannan bangare na duniya.