Hussaini Yero" />

Tsoffin Kansiloli 69 Sun Canja Sheka Daga APC Zuwa PDP A Zamfara

APC Zuwa PDP

Gwamna Bello Muhammed, Matawallen Maradun, ya karbi tsoffin kansiloli 69 da sakatarorin kananan hukumomi 14, wadanda su ka watsar da tsohuwar jam’iyyarsu ta APC zuwa jam’iyyar PDP a Zamfara.

Sakataren yada labarai na Gwamna Matawallen Maradun, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, ne ya bayyana haka a takardar da ya sanya wa hannu ya raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.
Kansilolin, wadanda su ka yi mulki a shekarun 2012 da 2015 zuwa 2019, dukkansu sun sauya sheka daga APC zuwa PDP karkashin inuwar kungiyar reshen jihar ta Zamfara.
Shugaban tsofaffin kansilolin, Alhaji Tukur Muhammad Magami, ya bayyana cewa, shawarar da su ka yanke na barin tsohon mai gidansu kuma tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari, ya biyo bayan imanin da su ke da shi game da salon shugabancin Gwamna Matawallen Maradun, musamman wajen yaki da ‘yan ta’adda da samar da tsaro da samar da kyakkyawan yanayin siyasa a cikin sassan jihar.
Alhaji Tukumar Magami ya ce, wannan gwamnatin da Matawallen Maradun ke jagoranta ta tabbatar da cewa,gwamnati ce ta kowa da kowa domin ba ta cin mutuncin ko barazanar siyasa ga ‘ya ‘yan wasu jam’iyyun siyasa adawa a jihar.
A cewar shugaban, “irin wannan gwamnatin na bukatar karuwa tare da tallafawar kowa da kowa, domin ta cigaba da samar da ribar dimukradiyya ga dukkan ’yan jihar.”
Kuma ya ba da tabbacin cewa. dukkanin mabiyansu da magoya bayansu har da danginsu su na da ra’ayi iri daya na sallamawa gwamnatin Matawalle kuma sun yanke shawarar komawa PDP tare da addu’ar samun dawamamen zaman lafiya a jihar baki daya.
Hakazalika, kakakin tsohon sakatarorin karamar hukumar, Alhaji Saadu Mayana, ya bayyana cewa, gamsuwa da yadda gwamna Bello Matawallen Maradun ya ke tafiyar da ayyukan cigaban jihar ya sanya su ka mika masa mubayi’ar su.
Kuma a madadin tsaffin sakatarorin kananan hukumomin 14 na jihar, sun yanke shawara baki daya sun dawo gwamnatin PDP a jihar karkashin Jagorancin gwamna Matawalle Maradun.
A nasa martanin, Gwamna Bello Muhammed Matawalle Maradun ya bayyana farin ciki sa a loakacin karbar sabbin masu shigowa PDP.kuma ya tabbatar da cewa,su masu san cigaban jihar Zamfara ba masu dakileta ba.
Matawalen Maradun ya bayyana cewa,’kofofin sa a bude ta ke ga kowa da kowa dan amsar shawarorin d a hanyoyin da su ka dace mubi wajan kawo ci gaban jihar.

Exit mobile version