Abba Ibrahim Wada" />

Tun Ina Yaro Na Ke Son Buga Wasa A Juventus – Ronaldo

Shahararren dan wasan kasar Portugal na kungiyar kwallon kafa ta Juventus Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa tun yana dan karamin yaro yake kallon kwallon Juventus kuma yake da burin watarana ya bugawa kungiyar wasa idan ya girma.

Ronaldo wanda yakoma kungiyar ta Juventus a watan daya gabata akan kudi fam miliyan 100 daga Real Madrid ya bayyana cewa bai dauki wani lokaci ba yana tunani lokacin da Jubentus tace tana bukatarsa daya koma kungiyar.

Dan wasan wanda ya shafe shekaru 9 a Real Madrid ya lashe kofuna da dama a rayuwarsa  ya bayyana cewa tun bayan da aka kammala gasar cin kofin zakarun turai ya yanke shawarar barin Real Madrid kuma Juventus ce kungiyar dayaga yakamata yakoma.

“Ina jin dadin zama na anan, magoya bayan kungiyar suna sona ‘likitoci suna sona shugabanni suna sona sannan ‘yan uwana ‘yan wasa suna nunamin soyayya saboda haka ina farin ciki sosai da kasancewa ta anan” in ji Ronaldo

Yaci gaba da cewa “Kungiyar Juventus babbar kungiya ce kuma tun in matashin dan wasa nake son buga wasa acikin kungiyar sannan kuma mun buga wasanni dasu da yawa kuma magoya bayan kungiyar suna sona duk da bana kungiyar”

Ronaldo dai ya buga wasanni 438 a Real Madrid sannan kuma ya zura kwallaye 450 tare da lashe kofin zakarun turai sau hudu da kofin laliga sau biyu sannan ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau hudu a kungiyar.

Exit mobile version