Jama’a barkan ku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin dake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau na dauke da sakon wata baiwar Allah wacce ta bukaci da a boye sunanta, inda sakon nata ya fara da cewa; “Dan Allah ina so a yi magan akan yara da ake kawo su Almajiranci duba da yanayin da ake ciki na yunwa, Allah raina yana baci a kan iyayen yaran yanzu ai ‘da’ da yanzu ba daya ba ne, yanzu rayuwa ta sauya komai ya yi zafi rayuwa ta yi tsada kowa takai-takai su kuma sun zamo abin tausayi, saboda na gidan ma basu samu ya wadace su ba bare su mikawa na almajirai. Iyayensu suna cutar da su wallahi saboda ba sa hado su da abin da za su ci koda na ‘6 months’ ne, sai ki ga yaro yana kuka saboda yunwa ya yi yawo bai samu ba, ga su yara kanana ba su san babu ba, ba su da lokacin da za su je su nemi kudi dan su ciyar da kansu, kai! Allah ya sa mu dace.”
- Gudunmawa 10 Da Ilimi Ke Bayarwa Ga Al’umma (2)
- Matsalolin Ilimi A Nijeriya Da Hanyoyin Gyara Su (1)
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me ya sa iyayen yara suke kai yaransu kanana karatu birni ba tare da sun hada da abin da yaran za su ci ba? Me hakan zai iya haifarwa/Wane matsaloli yaran ka iya fuskanta?
Ko ta wacce hanya za a magance matsalolin da almajirai ke fuskanta yayin da iyayensu suka kaisu birni domin yin karatu? Wacce shawara za a bawa iyayen yara musammn masu tura yaransu karatu zuwa cikin birni, har ma da su kansu malaman da suke karbar yaran? Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Halimatu Yusuf, Daga Jihar Kano:
Gaskiya ne rayuwar Almajirai a wannan zamanin innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un, gaskiya suna cikin wani hali na tausayawa, saboda yunwa ba abin da ba ta sawa. Yunwa za ta iya haifar musu da lalacewar tarbiyyarsu domin kome za su yi maka indai za ka basu abinci wallahi za su iya abin da aka saka su.
Ya kamata iyaye dan Allah dan Annabi Muhammad (saw) idan har ya zaman musu dole sai sun kai yaransu makarantar Allo to lallai su hada su da abincin da za su ci koda na rabin shekara ne, saboda wallahi summa’tallahi ranar gobe kiyama sai Ubangiji ya tsaida ku akan kiwon daya baku na ‘ya’yanku su kuma malamai su ji tsoron Allah su sani su ma akwai hisabi tsakanin su da dalibansu sai rashin lafiya ya kama yaro amma malami ba kulawa daga nan sakacin su ya sa yaro ya rasa ransa.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano LGA:
Maganar gaskiya abin da zan iya cewa akan wannan sam! yanzu duniya ta canja abar wannan layin domin a shekarun baya kai yara almajirta yana kawo gyara, amma ban da wannan zamanin. Rashin tausayi da sanin darajar yaran domin wasu yaranma idan ki ka bunkcika za ki ga iyayensu mata ba sa gidan uban yaran sannan abin da ya sa ba sa hada musu da abinci suna ganin tun asali haka ake yi amma yanzu rayuwar ta canja ba a samun abincin a wajen karatun.
Matsalolin suna da yawa amma babba daga ciki ita ce gurbatar tarbiyyar yaran da koyon rashin ji. Sabida ta nan yara suke koyon sata, shaye-shaye harkar daba da dai sauransu. Hanyoyin suna da yawa daya daga ciki ita ce iyaye suna daurewa suna hadawa yaran da kayan abinci kamar yadda ake yi a ‘boarding school’ sannan iyaye suna zuwa duba yaransu koda bayan wata 1-1 ne duba da ita bata boko bace balle ace sai ranar ‘bisiting’ ko afkuwar larura, kuma zuwan iyaye zai sa su kansu yaran suna nutsuwa su yi abin da ya kaisu haka shi ma malamin zai dinga kula da su sosai sabida ya san akoda yaushe uban yaran zai iya zuwa ganin dansa. Shawarata a nan ita ce dai abin da na kawo a sama malaman su shigo da tsarin kawo yaro da abin da zai dinga ci ko kudin siya idan har karatun ake so su yi ba yawon bara ko neman kudi ta kowacce irin hanya ba, haka su ma iyaye suna yawan zuwa duba yaransu a wanne irin hali yake?, Allah yasa mu dace amin.
Sunana Hassana Hussain Malami (Haseenan masoya) daga Jihar Kano:
Gaskiya a halin da muke ciki yanzu a Nijeriya abun ya ci tura wasu iyayen suna kai ‘ya’yansu almakjranta ne sabida ba su da yadda za su yi su ciyar da su tom sai ya zamana inda za a kai su nan ma babu abincin domin a halin da Ake yanzu a Nijeriya sai dai mu ce InnalillAhi wa inna ilaihi raji’un dan halin yunwa yayi yawa, mutanen cikin gidan ma wasu sai su yi kwana uku ba su dora abinci ba bare kuma har su samu su ci su bawa almajiri, wallahi! wallahi!! wallahi!!! ni na ga gidan da sai da aka yi sati biyu ba a dora tukunyar abinci ba to, kun ga kuwa ta ya almajiri zai samu ya ci su ma na gidan neman taimako suke yi ga shi yanzu almajiran yara kananu ake kawo wa wadanda ba za su iya futa su yi dako a kasuwa ba ko kuma aikin karfi Allah dai ya sa mu dace.
Wasu iyayen kuma wallahi suna da halin rike ‘ya’yansu amma tsabar zalunci yake hanasu rike su sai dai su tura su almakiranta daga lokacin da aka ce ruwa ya zuba damuna ta sauka sai ace su koma gida haka za su koma gida su yi aikin gona tsawon wasu watanni har a kwashe kayan amfani a gona, sannan a kuma turo su makaranta ba za a barsu su ci wannan hatsin ba sai dai su zo su yi ta yawo a hanya, gaskiya akwai laifin iyaye a ciki, ina mai ba su shawarar indai za ka iya rike ‘ya’yenka ka rike su a wajenka, akwai makarantun addini a garinku sai a saka yaro Allah ya sa mu dace.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Jihar Neja:
Gaskiya bai kamata ba, yawancin almajirai rashin abinci yana jefa su cikin wani irin hali wanda daga baya za su dawo su rika da sun sani idan suka girma, to a nawa tunanin suna kai yaransu sabida su samu saukin ciyarwa ne kawai, musamman yadda suke haifar yara barkatai babu sassautawa karshe kuma su zo abincin da za su ci ma yana gagararsu dana yaran shiyasa suke fakewa da za su tura yara birni karatu, sannan akwai kwadayin wane ya je birni yayi kudi ni ma bari na tura nawa duk wahalar da zai sha bayan wuya sai dadi, da dai sauran dalillan da su kadai suka bar wa kansu sani.
Matsalolin da yara za su rika fuskanta sunada yawa musamman wajen dauko dabi’a mara kyau wacce iyayensu za su yi kuka su yi da-sun-sanin kaisu. Shawara ga iyayen yara su rika haihuwa daidai karfinsu daidai abin da suke da shi wanda za su iya bawa yara tarbiyya har su saka su a makaranta ba wai kai su birni almajiranci ba dan yanzu kai ya waye na kauyen ma suna saka yaran a makarantar zamani.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To almajiranci wata hanya ce da’ake bi wajen neman ilimin karatun addini kuma magana ta gaskiya a shekarun baya ana samun ilimin karatun al’kur’ani sosai ta wannan hanya, to amma magana ta gaskiya yanzu matsaloli da dama sun mamaye wannan hanya wanda hakan ya sa al’amura suka lalace sosai.
To magana ta gaskiya a yanzu mafi yawan iyayen suna zabar wannan hanya ne domin ragewa kansu dawainiya ko daukar nauyin iyali ba wai don yaran su samu karatu ba, don haka nema ya sa idan suka kai yaran suka jefar ba sa kara waiwayarsu domin sanin halin da suke ciki.
To matsalolin da hakan yake haifarwa na da yawa, da farko karatun ma ba a samun sa yadda ya dace, ga kuma lalacewar tarbiyya, a wasu lokutan kuma malaman suna bautar da su ta hanyar sa su aikin karfi a gonakai da sauran gurare. To da farko dai gwamnatin ya kamata ta shiga cikin al’amarin dumu-dumu domin zamanantar da shi da kuma basu kulawar data dace domin inganta rayuwar yaran. To shawara anan ita ce; ya kamata iyayen dai su sani ‘ya ‘ya amana ce da Allah ya basu don haka dole za su yi bayani akan yadda suka tafiyar da al’amarin su, don haka ya kamata iyaye suyi iya kar bakin kokarinsu wajen kula da yaransu, Allah ya sa mu dace.
Sunana Fatima Tanimu Ingawa Daga Jihar Katsina:
Babban kalubale a wannan zamanin shi ne yawaitar barace-barace na kananan yara masu mafi karancin shekaru, sun gogu sosai da barar don na ci karo kwanaki da wani yaro karami da ake ma lakabi da “zakin-bara” saboda gwanancewa a maula. Kalubale ne babba a kan irin wadannan iyaye da suke tara yaran da ba za su iya lura da su ba, sai dai su turo su birane don neman kai da su sai su fake da cewar karatu suka turo su.
Ba kuma maganar basu abincin su taho da shi tunda daman rashin wadatacciyar cimar da za su kula da su ya sa suka turo su al’majiranci. Hakan na haifar da babbar matsala da ka iya jawo tabarbarewar tarbiyya, domin yunwa ba abun da bata sanyawa.
Ga kuma kalubale da dama da garkuwar jiki ke fuskanta sakamakon takurawa ta rayuwa. Hanya daya ce za a magance wannan, illa iyaka malamai su tsaya tsayin-daka na tabbatar da basu karbi kowane da ba face sai da gamsasshen tallafi daga iyayensa, kama daga abinci, tufafi gwargwadon hali, kudin magunguna (kiwon-lafiya), karamar katifa ta muhallin kwanciya, sabulan wanka dana wanki da dai sauraransu.
Baya ga wannan malamansu su yi kokarin daura su akan sana’o’in hannu da za su rika yi bayan tashi daga makaranta, wannan shi ne zai kawo mana sauyi mai nagarta.
Sunana Anas Bn Malik Achilafiya:
Tsakani da Allah bai dace iyaye suke tura ‘ya’yansu zuwa Almajiranci a wannan rayuwa da ake ciki ba, domin idan karatun addini ko haddar alkur’ani ka ke so yaronka ya samu, akwai makarantu na gwamnati, dana kudi da yawa da ake samu.
Haka kuma tura yara bara ko almajiranci baya rasa nasaba da wurgin kwallon mangwaro da wasu iyayen ke yi wa ‘ya’yansu, domin hutawa daga dawainiya da su. Kuma wallahi a karshe da yawa yaran ba karatu suke samu ba, sai dai tarbiyya ta lalace, su koma wata mummunar rayuwa (Allah kare).
Dan haka wannan nauyi na iyaye da gwamnati ne, iyaye su ji tsoron Allah su kula da amanar da Allah ya basu na ‘ya’ya har zuwa aurensu, sannan gwamnati ta ci gaba da kawo tsare-tsare domin tabbatar da makarantun Allo sun koma suna gogayya da na boko duba da bukatar hakan da alumma ke ciki. Har ila yau su ma malaman da suke karbar yaran, ya kamata su yi wa kansu tsari na kin karbar duk yaron da iyayensa ba za su dauki dawaniyar cinsa da shansa a lokacin da za su kawo shi da ziyartarsa lokaci-lokaci ba.
Sunana Aisha D. Sulaiman:
Har ga Allah bai dace ba idan muka lura yawanci ba a fiya daukar mutum daga birni ace wai an kai shi almajiranta kauye ba, daga kauyen ake dauko wa a kawo birni, ya kamata gaskiya iyayenmu na kauye a fadakar da su. Dauko yaran nan da ake a kawo su almajiranta ana tauye musu hakki ana cutar rayuwarsu saboda ba su samu sun ci ba, a haka wani zai tafi ya yi iskanci a bashi kudi wani ba zai ma yi karatun ba sai ki ga wasu kuma sun shirya gidan mata su yi tai musu aikace-aikace kawai dan a basu abin da za su ci masu dan dama fa kenan, wasu kuma sai dai su buge da sace-sace , dauke-dauke kuma duk dai musabbabin abin shi ne yunwa, bai samu ya ci abinci ba a rayuwar yanzu da muke fama na gidanma ya aka kare bare kuma ace har ka ci har yayi saura har ka bawa almajiri.
Har ga Allah ya kamata a duba su a yi kira ga iyayensu hakan ba daidai bane. Shawara kuma gaskiya su ma iyayenmu na kauye ya kamata idan ki ka haifi yaro ki dage gara ko wankau, dakau, da dai sauransu aiki na hannu wanda za ki iya ki yi ki ciyar da ‘ya’yanki da ki bari a kawo miki su gari baki san ya suka tashi ba, baki san ya suka kwanta ba, baki san wani irin hannu suke fadawa ba, wallahi wani yaron idan muka ganshi idan yanada kani ma dai daya ne ba zai wuce ace yanada kanne biyu ba to, me ya jaho haka dan Allah dan Annabi?, ‘ya’yan ne suka yi musu yawa?, a’a! ba za su iya tarbiyyar ‘ya’yan bane?, ni ina mamakin uba ya rabo da da iyaye wai an kawo almajiranci, ko sun yi musu yawa ne, ko ba sa su ne? oho! amma gaskiya ya kamata mu gyara mu dubi da wannan tsokaci da aka yi dan gaskiya yayi an kawo abin da za mu fadantu mu alfanantu.
Sunana Hassina Ahmad Daura:
Tabbas wallahi ni ma wannan abun yana bani haushi to dan Allah wannan rayuwar da ake fama mutane kowa yana ganin abun da yake gani ta ya ma za ka ci abinci amma yaronka bai ci ba kai kana gida ka dafa ka ba miji ka ba sauran yara ka tura wasu su je karatu bayan babu abin da za su ci, ni dai wallahi shawarata duba da yanayin da muke ciki rayuwa tayi wahala yanzu ba Almajiri ba ba ma yaran makota ko na ‘yan’uwa ma kana kasa basu alherin abinci saboda kai ma ba ka da shi a wadace taya Almajiri dan yayi bara zai samu?, kuma iyaye idan za su gani fa kafin a dauki abinci mai kyau kamar yadda kowa ya ci aba Almajiri akan dauko kanzo ko sauran na yara ko wanda ya fara lalacewa ko kuma idan suka yi maka aiki ka ba su ya Allah, shi fa ake basu gaskiya sai an duba an gane iyaye dan Allah muj a yaranmu a jikinmu yanzu duka rayuwa bata yi wa, ba za ka iya bawa yaranka tarbiya ba sai ka basu abinci, ba za ka taba sa yaronka aiki yayi maka ba sai ka bashi abinci, yaro ba zai je makaranta ba sai ya ci abunci yake iya karatu
wallahi yanzu komai ba zai yu ba sai da abinci ko biyayya yaron da ka haifa ba zai yi maka ba sai ka bashi abinci, Allah ya sa mu gane mu fi karfin zuciyarmu, Allah ya ba mu abin da za mu yi masu daga hala.
Sunana Hassana Sulaiman Hadejia. A Jihar Jigawa:
Maganar gaskiya dai gameda batun yau kan abin da ya shafi almajirci abu ne da ya kamata ayi duba sosai na tsanaki a kan lamarin, dan kowa gaskiya masu iyayen ma a gari wasu da dama wahala suke sha bare su da ba su da iyayen kusa da su. Kusan daga cikin abin da ya sa wasu daga cikin iyaye ke kaiwa yaransu almajirci shi ne babu ce ta sa har suke iya hakura da rayuwa da yaran nasu kusa da su shi ya sa suke kai su almajirci din, sannan kuma wasu suna kaiwa yaransu almajirci ne musamman iyaye matan da aka mutu aka barsu da yara hannunsu kuma rashin matallafi ke sawa su kai yaran nasu ga almajircin dan wasu iyaye matan da za su samu tallafi daga ‘yan’uwa babu yadda za su kai yaransu almajirci duba da soyayyar uwa da ‘ya’ya. Kusan daga cikin abubuwan da kai wa yaran zai iya haifarwa akwai; yara na zama tangararro, marasa tausayi, zama masu dauke-dauke, rashin maida hankali ga abin da ya kawo su suka bar gidajen nasu, fadawa ga hannun bata gari, rayuwarsu na iya shiga cikin hadari da sauransu.
To kusan hanyar da za a iya gyara wannan matsalar shi ne; dole sai gwamnati ta fara shigowa cikin lamarin, kuma ta hanyar da za ta iya tallafawa yaran nan shi ne samar musu da makarantun masu kyau ta samar musu da wani tagomashin kayan abinci duk wata, sannan kuma ta hanasu barace-baracen nan na kan tituna da gidajen mutane su kuma al’umma su ma akwai hanyar da za su iya taimakawa almajiran nan kamar daukar su agidajensu kana su maida su tamkar ‘ya’yansu na cikinsu kuma su sanya su a makarantun boko dana islamiyya idan aka yi hakan kusan za a samu sauyi ga lamarin. Shawarar da zan bada anan musamman ga su iyayen yaran anan ita ce; dan Allah idan yaran basu kai shekarun da za su iya yi wa kansu wasu abubuwan ba su yi hakuri da kai su almajirci, kuma su nemi wata ‘yar sana’ar da za su rika yi cikin gidajensu dan tallafawa yaran ba tare da sun tura su almajirci ba. Sannan kuma shawara ga malaman da ake kaiwa yaran nan shi ne; malaman da farko su ji tsoron Allah su kuma san yaran nan da aka kawo musu amana aka basu kuma Allah zai tambaye su kanta, dan haka idan suka yi wa yaran nan rikon da za su cutu za a tambaye su gobe kiyama.
Sunana Ummi Jos (YM Gidado):
Almajiranci dai abu ne da muka taso tun iyaye da kakani muka samu ana yinta, ma’ana mutum zai tashi daga garin da yake zuwa wani garin don neman ilimin addini. A kwai dalilai da yawa dake sa iyaye kai yaransu kanana almajiranta, misali; wani shi ma da ma yayi almajiranci a wajen ya sami iyali har yayi aure ya haihu kuma yanada yakinin cewa yaro baya samin ilimi da sanin rayuwa har sai ya je wani garin daban, wasu kuma talauci ne ke saka shi, ya haifi yaran da yawa kuma ba shi da karfin da zai iya rike su.
Gaskiya suna fuskantar munanan matsoli, akwai wadanda a dalilin haka suke rasa rayukansu, wasu kuma su fada sace-sace,sl shaye-shaye da munanan abubuwa ma,sl sabidda wahala da yunwa ba abin da bai sa yara. Duk kan wanda zai kai yaronsa almajiranci malamin ya tabbatar ya bada abin da yaro zai rika ci, sannan iyaye su tabbatar suna bibiyar yaransu da suka kai almajiranci koda kuwa ta wayar sadarwa ne suna kiran malaman suna hadaku da yaransu suna jin halin da suke ciki.
A karshe ina kira ga malamai da alaranmomin mu su sani duk wanda ya kawo maka amanar yaronsa almajiranci wajenka ka rike masa amana tsakaninka da Allah, kuma duk wanda ba zai kawo yaro da abin da zai ci ba kar ku karbi yaron.